1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Condoleezza Rice na kan hanyarta ta komawa Gabas Ta Tsakiya

July 29, 2006
https://p.dw.com/p/Buom
Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice na kan hanyar komawa yankin GTT, inda zata yi kokarin yin sulhu tsakanin Isra´ila da Libanon. Muhimmin batun da zata tattauna a wannan ziyara ta biyu cikin mako guda, shine game da tura dakarun kasa da kasa a kudancin Libanon. A ganawar da suka yi fadar White House shugaba GWB da FM Birtaniya Tony Blair sun nuna goyon bayan girke dakarun a wannan yanki. To amma shugabannin biyu sun yi watsi da batun tsagaita wuta nan take. Bush ya nunar da cewa da farko dole ne a warware matsalolin da suka janyo wannan rikici, wanda ya dora laifin sa akan kungiyar Hisbollah, yana mai cewa ita ce umul-aba´isin tabarbarewar halin da ake ciki a GTT.