1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COPA za ta mara wa Hama baya a zagaye na biyu

Mahamane KantaFebruary 27, 2016

Hadin gwiwar 'yan takara na bangaren adawan Nijar a zaben shugaban kasa zagaye na farko wato COPA 2016 ya jaddada goyon bayan ga dan takara Hama Amadou a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1I3O5
Niger Anschlag auf Hama Amadou Opposition
'Yan Adawan Nijar za su je gidan Hama AmadouHoto: Mahaman Kanta


Tun dai kafin zagaye na farko hadin gwiwar jam'iyyun na adawa da suka kafa wannan hadaka mai suna COPA suka sha alwashin mara wa duk wanda ya zo na biyu baya a zaben Nijar. Saboda haka ne suka jaddada wannan alkawari nasu inda suka ce a halin yanzu Hama Amadou ba dan takarar jam'iyyar Moden FA Lumana Afrika kawai ba ne, amma dan takara ne na COPA 2016 kuma za su yi yakin neman zabe tare da shi.

Mun samu labarin cewa, akwai kuma wasu daga cikin 'yan takaran da suma za su yanke shawarar shiga wannan gungu na 'yan adawa ya zuwa yammacin wannan rana ta Asabar. Sai dai a hannu daya hadin gwiwar 'yan adawar ya ce zai kalubalanci sakamakon da aka bayar na wasu yankun a zagaye na farko na shugaban kasa da na 'yan majlisa.