1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corea ta Arewa, ta ce a shirye take ta daina gwajin makamin nuklea

October 22, 2006
https://p.dw.com/p/Buf1

Wani labari da jaridar Yonhap ta buga, a sahiyar yau lahadi , ya nunar da cewa, hukumomin Corea ta Arewa, a shirye su ke su dakatar da aniyar su ,ta yin wani saban gwajin makamin nuklea, amma fa, da sharaɗin Amurika, ta cire ƙaffan zuƙar da ta azawa kasar.

Jarida ta ce, hukumomin, sun ɗau wannan alkawari, albarakacin ziyara aikin da wakilin Sin, Tang Jiaxua, ya kai Pyong Yang, a makon da ya gabata.

Sannan hukumomin,sun bayyana aniyar komawa kann tebrin shawarwari, da ƙasashe masu shiga tsakani, amma in Amurika, ta amince ta ɗage takunkumin karya tattalin arziki, da ka ƙargamawa Corea ta Arewa.