1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corea ta Arewa ta yi watsi da tayin dakatar da shirin ta na nuklea

July 13, 2006
https://p.dw.com/p/Buql

Sati ɗaya bayan harebe- harben makamai masu lizzami, da Corea ta Arewa ta yi, yunƙurin sassanta rikicin, da ƙasar Sin ta shiga, bai cimma buri ba.

Christopher Hill, wakilin mussamman na Amurika, a wannan tantanawa, ya bayyana wannan sanarwa.

A washe garin harba makamman, ƙasar Chine, da ke da alaƙa da dangatar ƙut da ƙut, da Corea ta Arewa, ta yi tayin shiga tsakani.

Saidai tantannawar da aka yi, tsakanin ɓangarorin daban-daban, ta kasa samun nasara ciwo kan hukumomin Pyong Yang.

Christopher hill ya yi rangadi a ƙasashen Corea ta kudu, Japon da Chine, domin ɗaukar mattakin bai ɗaya, a game da abinda ya kira tsageranci, da hukumomin Corea ta Arewa ke nunawa dunia.

Amurika ta kasa cimma nasara, dalili da goyan baya da Corea ta Arewa ke samu, daga ƙasashen Chine da Rasha, wanda su ka yi barazanar hawan kujera naƙi a komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, a game da matakan hukunci,da ake buƙatar ɗauka kan Kora ta Arewa.