1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cote D´Ivoire ta yi saban Praminista: Charles Konan bani

December 5, 2005
https://p.dw.com/p/BvHs

Bayan wata da watani na cece kuce, a karshe ,kasar Cote D´Ivoire ta samu saban Praminista.

A ranar jiya ne, shugabanin kasashe Afrika masu shiga tsakanin rikici kasar su ka bayana sunan Charles Konan Bany, tsofan gwamnan babban bankin kasashen yammacin Afrika, a matsayin wanda, zai maye gurbin Seydu Diara.

Masharahanta na hasashen cerwar, saban praministan na da babban aiki a gaban sa, na shirya, zabe, nan da watani 10 masu zuwa, a wannan kasa da ke fama da rikicin tawaye.

Kazalika, baban kalubalne da zai fuskanta shine na kwance damara yaki ga yan tawaye, da kuma dakarun sakai masu goyan bayan shugaba Lauran Bagbo.

Saidai alamomin farko, na nuni da cewa za shi cimma nasara, ta la´akari da yada shugaban kasa Lauram Bagbo da Jami´yun adawa, da kuma yan tayawe, gaba daya su ka amincewa da saban Praminstan.

Kasashe da kungiyoyi daban daban na dunia, su fara bayyana gamsuwa da matakin da a ka cimma na warwate rikicin kasar Cote D´Ivoire.

Faransa da ke da da soji dubu 3 a kasar ta jinjina damtse ga bangarori daban daban masu gaba da juna, ta kuma bukaci su ba marada kunya, ta hanyar ba saban Praminstan goyan baya.