1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cuba ta kudri aniyar yakar sauro a kasar

Salissou BoukariFebruary 22, 2016

Shugaban kasar Cuba Raul Castro ya sanar da daukan matakan kawo karshen sauron da ke haddasa cutar Zika da ake fama da ita a wasu kasashen yankin Latin Amerika.

https://p.dw.com/p/1I04q
Kuba Präsident Raul Castro
Raul CastroHoto: picture alliance/AP Photo/D. Boylan

Shugaban ya ce za a yi amfani da sojojin kasar 9000 domin cimma wannan buri na kishin sauro, da kuma samar da tsafta duk kuwa da cewa ba a samu bullar cutar ba a kasar. Bayan ma sojojin akwai kuma 'yan sanda 200 da za a yi amfani da su wajan wannan aiki. Ana zaton kwayar cutar ta Zika dai na haddasa canjin halittar jarirrai ta hanyar mayar da su masu kananan kanu. Shi dai wannan sauro mai sanya kwayar cutar ya haddasa cutar a cikin kasashe a kalla 36 daga cikinsu 28 na yankin Amirka ta Arewa da kuma ta Kudu.