Cunkoson Pasinjoji a filayen Jiragen sama
April 21, 2010Talla
Kwanaki shida bayan bazuwar Toka daga Dutse mai amon Wuta, wayewar garin yau laraba, an buɗe mafi yawan filayen sauka da tashin jiragen sama da ke nahiyar Turai. Ƙungiyar masu kula da sufurin sama a Turai ta sanar da cewar, kimanin jirage dubu 28 ne zasu fara tashi kamar yadda aka saba. Kazalika Jamus ta sanar da buɗe dukkan filayen sauka da tashin jiragen saman dake faɗin ƙasar. Tun a jiya ne dai jiragen kamfanin Lufthansa na tarayyar ta Jamus, suka fara zirga-zirga, sai dai har yanzu filayen jiragen saman na fama da cunkoson pasinjoji, sakamakon tsaikon harkokin sufurin sama, daga tokar amon wutan na ƙasar Iceland.
Mawallafiya- Zainab Mohammed