1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Cutar hanta ta bulla a Jamhuriyar Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
April 20, 2017

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da bullar cutar nan mai suna Hépatite E da ke da nasaba da hanta wanda har ta yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 25 a yankin Diffa da ke kudu maso gabashin kasar,

https://p.dw.com/p/2bclf
Gabun Albert Schweitzer Krankenhaus in Lambarene
Hoto: DW/J.-P. Scholz/A. Kriesch

Ministan kiwon lafiya na Jamhuriyar Nijar Dakta iassou Idi Mainassara ya ce daga ranar da cutar ta bulla zuwa kawo yanzu an samu akalla mutun 86 da suka kamu da it wanda tuni mutum 25 daga cikinsu sun rigamu gidan gaskiya musamman ma a yankin Diffa din inda nan ne aka samu bullarta.

Tun a tsakiyar watan jiya ne dai hukumomin lafiyar yankin suka fara lura da bullar matsalar kuma bayan kaddamar da bincike hukumomin suka gano cutar hanta ce mai saurin kama jama’a ta hanyar shan ruwan da ya ke dauke da kwayoyin cutar da kuma ke saurin halaka mata musamman masu juna biyu.

Tuni dai gwamnatinNijar din ta bakin ministan kiwon lafiya ta ce ta dauki wasu muhimman matakai don kare jama'a daga kamuwa da cutar inda minitan ya ce ''mun kafa wani kwamitin da ya kumshi daukacin ministocin da ke kula wa da ruwa da noma da kiwon da ma’aikatar muhalli don tunkarar matsalar. Mun kuma kafa wasu kwamitoci biyu daya na kasa baki daya game da cutar daya kuwa a yankin Diffa tare da tsarin gaggawa na tunkarar cutar a yankin Diffa''.

Masan kiwon lafiya a Nijar dai sun shiga fadakar da jama'a kan yadda ake kamuwa da wannan cuta. Malam Moumouni Mahamane da ke zaman kwararre ne a ma’aikatar yaki da annoba a ma’aikatar kiwon lafiyar na Jamhuriyar Nijar ya ce "na farko akwai masassara da ciwon kai da sauyawar kalar ido da amai da kuma ciwon ciki. Mata kuwa suna jin ciwo a mara kuma ciwon ya na sa fitsari mai kalar rawaya sannan ciwo ne da ke kashe mata masu juna biyu da gaggawa''.