1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar murar tsuntsaye a Turkiyya

Ibrahim SaniJanuary 10, 2006

Turkiyya ta tashi haikan wajen yakar cutar murar tsuntsaye a fadin kasar baki daya.

https://p.dw.com/p/BvU1
Hoto: AP

Ya zuwa yanzu bayanai daga kasar ta Turkiyya na nuni ne da cewa mutane kusan 100 ne a yanzu haka,ke jiran a gudanar da gwaji a kann su don tantance ainihin gaskiyar suna dauke da kwayar cutar ta murar tsuntsaye nau´ín H5N1 ko kuma a´a.

Daga dai cikin wadannan mutane, akwai mutane goma da suka fito daga babban birnin kasar wato Istanbul.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa matukar aka sami daya daga cikin wadannan mutane goma dauke da kawayar cutar,to babu makawa cutar mai nau´in H5N1 ta fara bulla a daya daga cikin manya manyan birane a kasar.

Ya zuwa yanzu dai an gano mutane 14 dauke da kawayar cutar ta murar tsuntsaye nau´in H5N1, ciki kuwa har da yaran nan uku yan gida daya da suka rasa rayukan su a makon daya gabata.

Duk da cewa wadannan yara sun rasa rayukan nasu ne a sakamakon kamuwa da wannan cuta ta murar tsuntsayen, daya daga cikin jami´an hukumar lafiya ta duniya wato Klaus Stöhr,cewa yayi babu tabbacin cewa wannan cuta ta fara yaduwa daga mutum izuwa mutum.

Rahotanni dai sun nunar da cewa yanayi na bullar cutar murar tsuntsayen a kasar ta Turkiyya na kamanni da irin bullar ta a kasar Vietnam, kasar data fita zaka a cikin kasashen duniya a game da fuskantar wannan matsala ta cutar murar tsuntsayen.

Masana ilimin kimiyya dai sun yi nuni da cewa matukar wannan cuta ta fara bulla daga nan izuwa nan a jikin yan adaman to babu shakka zata yi illa babba.

Da alama dai wannan sabon yanayi da kasar ta Turkiyya ta fada a ciki ya fara addabar yan kasar, a misali Osman Ayik, daya daga cikin masu gudanar da aiki a guraren shakatawa a kasar cewa yayi ba a da bayan asarar rayukan akwai kuma asarar kudaden shiga da kasar take, a sabili da cewa da yawa daga cikin masu yawon shakatawa izuwa kasar sun dakatar da yin hakan a halin yanzu.

Idan dai za a iya tunawa,tuni kasashen Russia da Biritaniya inda yan yawon shakatawa izuwa kasar ta turkiyya suka fi yawa, suka gargadi yan kasar tasu dasu dakata da hakan a halin yanzu har zuwa lokacin da komai zai dawo yadda yake ada.

Tuni dai kungiyyar gamayyar turai, wato Eu ta bayar da umarnin daina shigowa da tsuntsaye da kuma dabbobi cikin mambobin kasashen ta daga kasashe shidda da suka yi makotaka da kasar ta Turkiyya a matsayin rigakafi wanda hausawa kance yafi magani.

Kungiyyar ta Eu tace in har ya zama dole a shigo da abubuwa a cikin kasashe yayan nata, to dole ne sai an tantance lafiyar su tukuna.

A kokarin da hukumar lafiya kuwa keyi na dakile yaduwar wannan cuta, tuni ta aike da jami´an ta izuwa kasar ta Turkiyya don kalailaice irin halin da ake ciki, bisa manufar sanin matakin daya kamata a dauka a nan gaba.