1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar zazzabin Lassa ta bulla a kasar Benin

Salissou BoukariFebruary 2, 2016

A kalla mutane tara ne suka rasu da cutar zazzabin Lassa a kasar Benin daga cikin mutane 20 da ake tsammanin sun kamu da wannan cuta a kasar a cewar kungiyar UNICEF.

https://p.dw.com/p/1HoHb
Ebola in Sierra Leone überwunden
Hoto: imago/Xinhua Afrika

Wata sanarwa da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya fitar, ta ce mutun na farko mai dauke da cutar zazzabin na Lassa, an gano shi ne tun a ranar 05 ga watan Janairu a babban asibitin St Martin da ke Papané cikin karamar hukumar Tchaourou da ke a nisan kilomita 350 a arewacin birnin Cotonou. A cewar Dr Bagou Yorou kawo yanzu dai wannan asibitin na Tchaourou da kuma birnin Cotonou ne aka samu masu wannan cuta.

A watan Octoba na shekarar 2014 ma dai a kasar ta Benin an fuskanci wannan cuta ta zazzabin Lassa.