1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da akwai alamun kawo karshen yajin aiki a Guinea

January 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuTD
Shugaban Guinea dake shan matsin lamba ya amince ya nada sabon FM mai cikakken iko. Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin shugaba Lansana Conte da shugabannin kungiyoyin kodago ka iya kawo karshen wani yajin aiki na makonni biyu wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 60. Tun a ciki watan afrilun shekara ta 2006 kasar dake yammacin Afirka ba ta da wani FM bayan da shugaba Conte ya sallami shugaban gwamnati. A lokacin da dubban ´yan kasar suka fara zanga-zangar nuna adawa da wahalhalun da suke ciki a ranar 10 ga watannan na janeru, shugabannin kungiyoyin kodago sun nema da a nada sabon FM. Wasu kuwa sun yi kira ga shugaba Conte da ya sauka. Tun a shekarar 1984 Conte ke shugabantar kasar ta Guinea.