1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da alama an kawo karshen yakin basasar kasar Sudan...

December 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvGd

Mutanen kasar Sudan a kalla dubu dari biyar ne ake sa ran zaso dawo izuwa gida bayan da suka yi gudin hijira izuwa wasu kasashe kusan shekaru ashirin da suka gabata.

A cewar hukumar kula da yan gudun hijira ta Mdd, yan gudun hijira 150 ne dake zaune a matsugunan da aka tanadar musu a arewa maso yammacin kasar Kenya, za a fara dawo dasu izuwa kasar ta Sudan a karshen wannan mako da muke ciki a matsayin zangon farko.

Wannan yunkuri a cewar hukumar ta masu kula da yan gudun hijirar na a matsayin alama ce ta kawo karshen yakin basasar da kasar ta fuskanta na tsawon shekaru 21 da suka gabata.

Rahotanni dai sun nunar da cewa, ragowar yan gudun hijirar daga kasar ta Sudan na zaune ne a kasashe irin su, Uganda da Habasha da Congo da kuma Kenya. Ragowar kasashen sun hadar da Eritrea da Masar da kasar Afrika ta tsakiya.