1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Da alama Sudan zata amince da kara wa´adin aikin sojojin Afirka a Darfur

September 19, 2006
https://p.dw.com/p/Buj4

An fara ganin alamun cewa za´a kara wa´adin aikin sojojin da kungiyar tarayyar Afirka AU ta girke a lardin Darfur dake yammacin Sudan. To sai dai har yanzu ba´a tantance ba game da kudi da kuma kayan aikin da za´a bawa sojojin kiyaye zaman lafiyar. Mataimakin shugaban kasar Sudan Ali Osman Taha ya nuna goyon baya ga kara wa´adin aikin sojojin har bayan ranar 30 ga watannan na satumba. A cikin wani rahoto da ya aikewa kwamitin sulhu, wakilin MDD a Sudan Jan Pronk ya goyi da bayan tallafawa dakarun na kungiyar AU, muddin gwamnatin Sudan ta ki amincewa da girke dakarun MDD a lardin na Darfur. Mista Pronk ya fadawa wani taron manema labarai cewa mahukuntan birnin Khartoum sun nuna alamar amincewa da girke sojojin kasashen Indiya ko Pakistan a Darfur. Kasashen biyu dai na da sojoji a kudancin kasar ta Sudan.