1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

161110 Obama Karsai

November 16, 2010

Somamen dare a ɓangaren Dakarun Amurka na yin tasiri inji Amurka

https://p.dw.com/p/QAjD
Hoto: AP

Sannu a hankali dai Amurka na son janye Dakarunta daga cikin ƙasar Afganistan, sai dai shugaba Hamid Karzai  na tafiyar hawainiya dangane da hakan. Gabannin taron ƙungiyar tsaro ta NATO da zai gudana a Lisbon tsakanin 19 zuwa 20 ga wata, shugaban Amurka Barak Obama ya jaddada dabarun Amurkan a Afganistan.

Ba safai Kommandan rundunar Amurka da ke Afganistan General Peträus kan nuna ɓacin ransa da  shugaban afganistan ɗin ba. A ƙarshen makon daya gabata ne dai jaridar Washinton post ta Amurka ta yi hira shugaba Hamid Karzai, inda yayi magana ba wai dangane da gaggauta janye dakarun Amurkan kaɗai ba, amma har da bukatar janye masu yawan gaske. Karzai dai ya soki dabarun yaƙin na General Peträus, bisa yadda rundunar Amurkan na musamman ke kai somame cikin dare a cibiyar yankin 'yan Taliban.

Somamen na dare dai ya kasance matsala ta dindindin a ɓangaren rundunar Amurkan. Dangane da haka ne a hirar tasa da Washington Post shugaba Hamid Karzai yayi kira ga gwamnatin Amurka da komandan rundunar sojin Peträus, dasu taimaka wajen kawo karshen wannan matsalar.

Hillary Clinton in Phnom Penh Kambodscha
Hoto: DW

General Peträus dai yayi mamaki tare da nuna takaicinsa dangane da wannan suka na shugaban Afganistan. Wanda a cewarsa hakan zai gurgunta manufofin ƙungiyar tsaro ta NATO a ayyukan da suke yi a Afganistan.

Somamen na dare dai  a cewar komandan rundunar Amurkan dake Afganistan,  haifar da kyakkyawan sakamako, ta hanyar ƙaruwar kashe-kashe da cafke ƙarin shugabanin Taliban da ke wannan yankin. Ita ma Sakatariyar harkokin waje ta Amurka Hillary Clinton ta mayar da martani dangane da kalaman na Karzai...

"Wannan babbar gwagwarmaya ce, wanda yayi matukar tasiri da jagoranci mai ma'ana"

Clinton ta jaddada cewar dukkan ayyukan da rundunar Amurkan na musamman ɗin ke aiwatarwa, bisa da yawun kawance da ke tsakanin su  da gwamnatin Afganistan ne.

Ta kara da cewar ba wai Dakarun Amurkan su kadai ne ke kai waɗannan somame ba, suna fita ne tare da takwarorinsu na Afganistan, wanda kamar su ne ke nuna musu hanya. Duk da cewar Karzai ya koka da yawan jama'a farar hula da ke rasa rayukansu, ya zamanto wajibi waɗannan Dakaru na musamman su gudanar da ayyukansu, inji Clinton.

" Anfani da hanyoyin basira wajen yaƙar mayakan Taliban da sauran maɓuyansu  shine babban manufarmu na tafiyar da wannan somame"

David Petraeus / USA / Afghanistan / NO-FLASH
Hoto: AP

A yayinda a daidai lokacin zaɓen zaɓen shugaban ƙasa a Amurka a 2012, Dakarun Amurkan zasu janye daga yankunnan kudancin Afganisatan ɗin mai hatsari, kafin wannan lokacin an gurguntar da 'yan Taliban, ta yadda Dakarun Afganistan ɗin zasu jagoranci yankin.

Gabannin taron  na Lisbon dai Obama cewa yayi tsokaci da cewar

"Ya zamanto wajibi mu inganta ƙarfin hukumomin tsaron Afganistan da gwamnati, domin su samu damar ƙarɓar ragamar makomar ƙasar nan gaba."

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar Edita: Mohammad Nasir Awal