1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dabi'ar kona gawar mamaci na yaduwa a Ghana

November 9, 2016

A kasar Ghana sannu a hankali dabi'ar kona gawar mamaci na maye gurbin al'adar binne gawa da aka sani a kasashen Afirka shekaru da dama

https://p.dw.com/p/2SQ2J
Sierra Leon Ebola Beerdigung Opfer 14.08.2014
Hoto: AFP/Getty Images

A kasar Ghana dabi'ar kone gawa na neman kauda tsowuwar al'ada ta yin sutura da aka saba shekara da shekaru a kasashen Afirka, inda a yanzu ake samun al'umma da ke barin wasiya ga iyalansu na ba da umarnin a kone gawarsu bayan sun mutu. Bincike dai ya nuna cewa karanci da tsadar filin binne mamaci na daga cikin dalilan da ke sa dabi'ar kone gawar yin tasiri a Ghana.

 

A kasar ta Ghana, sannu a hankali ana samu mutanen da ke barin wasiyar yadda za'a binnesu da ma inda suke so a binne gawarsu. Wannan al'amari dai na zama wani sabon salo ne da ke neman kauda tsohuwar al'adar yadda aka saba binne mamata cikin rami ko a akwatuna kamar yadda aka saba gani a kasashen Afirka. Asiedu Mante, tsohon mataimakin babban bankin kasar Ghana ne da ke cikin wadanda suka bar wasiayar kone gawarsu bayan sun rasu.

 

"Ruhin da ke tattare da kai tamkar wani haske ne, wanda ke tare da ni tsawon shekaruna da nake da su 75 a yanzu. Idan kana yawaita ibada, hakanan gangar jikinka ke samun yawaitar haske. A don haka hanya mafi dacewa ta kyautata wa wannan haske da ke jikinka shi ne a banka masa wuta bayan ka mutu."

 

Afrika Obama besucht Kenia
Hoto: picture alliance/AA/Y. Juma

Ko a shekaru 10 da suka gabata, da wuya ake samun mutane da irin ra'ayin Asiedu Mante da ke son a kona gawarsu. To sai dai wannan tsari na kona gawa a Ghana, na ci gaba da yin tasiri a tsakaninn al'umma. Godfred Otu, guda ne daga cikin masu aikin kona gawa.

 

"Tsarin na ci gaba da samun karbuwa, saboda na farko dai akwai karancin filayen binne gawa, sannan wasu na alakanta tsarin da addini wanda suke ganin a yanzu yana shudewa "

 

Nii Arte Anum, na cikin masu aikin ginin ramin kabari a babban gidan mutuwar kasar Ghana, wanda ke cewa a yanzu dai ba kasafai ake samun wadataccen fili da za'a tona sabon kabari ba.

 

"A shekarun baya, ana binne mutane ba tare da sanya alama ba, bayan shekaru 10 ko fiye suna bacewa, amma a yanzu ana sanya alama a kan kaburbura wanda hakan ke cike filayen. Idan aka kwatanta da yadda ake kona gawa yanzu akwai sauki sosai, ganin tsarin binne mutum a kabari na cin kudi dala dubu biyar wanda za ayi tono, plasta akwati da allon alama da duwatsun girmamawa a kan kabarin. Amma dala dubi 2 ne kacal zai isheka a kona gawa."

 

Symbolbild Opfer der ADF
Hoto: Getty Images/AFP/K. Mailro

To sai dai duk da sauki da arhar da ke da akwai wajen kona gawa, amma ba kowane dan Ghana ba ne ya amince da tsarin a kona shi bayan mutuwa, duk da cewa wasu na kokawa kan yadda shuwagabannin gargajiya da mahukunta ke kankame filayen kaburbura, kamar yadda Douglas Agyeman Kusi ke cewa:

 

"Sam sam, a gaskiya bana ra'ayin gawata ta zamo toka. Ban yi amanna da shi ba a matsayina na dan Adam ina burin iyalaina su rika ganin kabarina suna tunawa da ni, ai ko da Yesu Almasihu ba a kona gawarshi ba."

 

Masu ra'yin tsarin kona gawa a kasar Ghana dai, na cewa akwai bukatar wayar da kan al'umma da zai sauya akidar jama'a da su karkata zuwa tsarin na kona gawa.