1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daga ina Afirka ta samo asalin sunanta

August 3, 2009

Taƙaitaccen bayani game da yadda Afirka ta samo asalin sunanta.

https://p.dw.com/p/J2t4
Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka Moammar Gadhafi yana tsaye a gaban taswirar nahiyar AfirkaHoto: AP

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Maisudan Halliru Abububakar daga jihar Kogi a tarayyar Najeriya. Malamin cewa ya yi; Shin daga ina nahiyar Afirka ta samo asalin sunan da ake kiranta da shi wato "AFIRKA"?

Amsa: Binciken da muka gudanar ya tabbatar mana da cewa, akwai ruwayoyi da dama da ke nuna yadda nahiyar Afirka ta samo asalin sunanta na Afirka ɗin, to amma dai ruwaya mafi shahara da kuma karɓuwa a tarihi ita ce, wadda ke cewar, sunan Afirka ya samo asali ne daga kalmar Misirawa ta "Afru-ika" wadda ke nufin "Ƙasar Haihuwa". Idan mutum ya kira kansa ɗan Afirka ko Ba'afirke, hakan na nuni da yadda mutum yake danganta sunansa da nahiyar Afirka a matsayin mahaifarsa. Kamar dai yadda bisa al'ada, idan mutum ya fito daga Amirka, sai a kira shi Ba'amirke, ko kuma idan daga Turai mutum ya fito sai a kira shi Bature. Hakama wanda ya fito daga ƙasashen Larabawa sai a kira shi Balarabe da dai sauransu.

Zwölfter Gipfel Afrikanische Union
Zauren taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka da ke birnin Addis Ababa na ƙasar HabashaHoto: picture alliance / Photoshot

Wani abu da ya kamata masu sauraro su fahimta shi ne, duk da an ce sunan Afirka ya samo asali ne daga harshen mutanen Misra, to ba ana nufin harshen Larabci tsantsa ba. Domin dukkanin ƙasashen da ke magana da harshen Larabci kowannen su yana da irin nasa karin harshen, amma tsantsar Larabci na nahawu wanda aka fi sani da 'FUSHA', Larabci ne da harshen alƙur'ani ya zo da shi.

Babu shakka haka batun yake, kuma dalilin da ya sa ma sunan Afirka ɗin ya samu daga harshen Misiranci shi ne, kasancewar shi harshen Misirancin yana da tasiri sosai akan harasa na asali kamar su harshen Girka da na Latin, kodadai dukkaninsu ana kiran su da suna harasa 'yan asalin indiya da Turai, wato 'Indo-European languages', a Turance kenan. Kuma ita kanta kalmar ta 'Indo' ta samu ne da kalmar Indiya, kuma ita kalmar Indiya ta samu ne daga wajen Larabawa lokacin da suka mamaye yankin na Indiya ɗin. Bayan da suka gano cewa Wani mutum da ake kira Kush ɗan Ham, yana da 'ya'ya biyu masu suna "Hind," da "Sind." To shi Hind ɗan Kush sai ya kafa daula a Indiya, shi kuma 'Sind' ɗan Kush sai ya kafa daula a yankin Larabawa. To daga nan ne Larabawa suke kiran al'ummar Indiya da suna 'Hindu'.

Tarihi dai ya nunar da cewa, tasirin da harshen Misarawa yake da shi a duniyar Larabawa da ma wasu yankuna na Afirka ya samu ne sabo da yawan fina- finai da wasannin kwaikwayo da kuma waƙe-waƙen mutanen misra da suka cika yankin. Sannan kuma kamar yadda Misirawa suke kiran mutanen da suka fito daga yankin Afirka da "Afru-ika" Su kuma mutanen Latin suna kiran afirkawan ne da nasu harshen inda suke cewa da su "Africanus" Wadda ke nufin daga Afirka". To amma kuma an fara amfani da kalmar Afru-ika lokaci maitsawo kafin a fara amfani da ta Africanus. Domin kuwa tun shekaru 400 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihis-salam, har zuwa shekaru 400 bayan komawar sa ga Allah, Rumawa sun kasance ne a arewacin Afirka. Su kuwa Girkawa sun kasance ne a Misira daga wajejen shekaru 300 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam, zuwa kimanin shekaru 200 bayan komawarsa ga Allah.

Karte Afrika deutsch Kongo Kinshasa
Ga taswirar nahiyar Afirka nan a ɓangaren hagu

Don haka ita kalamar 'Afru-ika" wadda ke ma'anar ƙasar haihuwa, kamar yadda ya zo a ɗaya daga cikin litattafan masanin tarihinnan Dr. Van Sertima, tana daga cikin kalmomin da suka samo asali daga harshen Misrawa, kuma shi harshen misirawa yana cikin "harsuna 'yan asalin Afirka da Asiya" Waɗanda aka fi sani da "Afro-Asiatic" languages, a Turance. Kuma sun haɗa da harshen Hebrew, da Larabci, da harshen Geez da kuma Armaniyanci. To amma fa duk da haka akwai wani ƙaulin da ke nuna cewa, asalin kalmar ta Afirka na da alaƙa da ita kanta nahiyar ta Afrikan, inda a cewar wasu 'yan afrika ɗin, kalmar na da alaƙa da wasu ƙabilu da ake kira Galla a ƙasar Habasha, wanda a harshensu kalmar "APRAKA" na nufin "Wuri mai tsananin zafin rana".

To a taƙaicen taƙaitawa dai zance mafi shahara game da asalin yadda sunan Afirka ya samo asali, shi ne wanda Dr. Van Sertima, ya faɗi a cikin littafinsa, inda ya ce sunan na Afirka ya zo ne daga kalmar Misranci ta 'Afri-uka" wadda ke ma'anar "Ƙasar haihuwa" wato "Motherland," kenan a Turance. Wanda kuma wannan laƙani na "Motherland," har yanzu ana amfani da shi idan mutum yana so ya danganta kansa da Afirka.

Mawallafi: Abba Bashir

Edita: Muhammad Nasir Awal