1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DAGULEWAR HARKOKIN SIYASA A ITALIYA.

April 21, 2005

faraminista Silvio Balusconi da ministan harkokin wajen kasar

https://p.dw.com/p/BvcM
Hoto: AP

Bayan mika takardar murabus din faraminista Silvio Balusconi ga shugaban kasar italiya a jiya laraba,a cewar bayanai da suka iso mana a yanzu haka shugaban Carlo Azeglio ya fara tattaunawa da shugabannin siyasar kasar bisa manufar kokarin kafa sabuwar gwamnati.

A dai gobe juma a ne ake sa ran shugaba Carlos zai gudanar da taron kolin a tsakanin sa da wakilan jamiyyun kasar baki daya,a kokarin da ake na kafa sabuwar gwamnatin.

A dai wan nan sabuwar gwamnati da ake shirin kafawa ana sa ran Silvio Balusconi zai ci gaba da rike wan nan mukami a matsayin faraministan.

Ya zuwa yanzu dai bayanan sun shaidar da cewa matukar Balusconi ya gagara kafa sabuwar gwamnatin to ala tilas shugaban kasar zai kira a gudanar da zabe na gama gari shekara daya kafin lokacin da aka tsayar.

Ya zuwa yanzu dai faraminista Balusconi ya kasance shugaba dake rikon kwarya kafin kafa sabuwar gwamnatin,to amma a daya hannun yana ci gaba da tattaunawa da ragowar jamiyyun hadin gwiwar don kafa wata sabuwar gwamnatin.

Daukar matakin yin murabus din daga bangaren Balusconin yazo ne a dai dai lokacin da jamiyyar sa ta fada cikin wani wadi na tsaka mai wuya sakamakon janyewar daya daga cikin jamiyyun hadakan tayi a makon daya gabata daga cikin gwamnatin hadin giwar da yakewa Jagoranci.

Kwanaki kadan kuma sai daya jamiyyar hadin gwiwar itama tayi kurarin janyewa daga cikin gwamnatin hadakar da Faraminista Silvio Balusconi kewa jagorancin.

Wadan nan abubuwan ne suka taru suka jefa gwamnatin cikin rudani na halin kaka ni kayi,wanda Ala tilas ya haifar faraminista Silvio Balusconin yayi murabus daga mukamin nasa.

A waje daya kuma rahotanni sun shaidar da cewa wadan nan abubuwan na faruwa ne a sabili da kangi na tattalin arziki da mutanen kasar ke ciki,wanda suke hasashen cewa watakila matzakan da gwamnatin sa ke dauka ne ya janyo musu fadawa cikin wan nan balahira.

Ya zuwa yanzu dai jamiyyun UDC da An da sukaýi kurarin ficewa daga gwamnatin Hadakar a yanzu haka sun nuna amannarsu ta shiga cikin sabuwar gwamnatin da Silvio Balusconi zai kafa nan bada dadewa ba.

To amma hakan a cewar jamiyyun zai faru ne kawai matukar idan gwamnatin ta Balusconi zata aiwatar da sabbin matakai da suke bukata a hannu daya kuma da gudanar da sauye sauye ga ma,aikatun kasar.

Ibrahim Sani.