1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

daidaituwa tsakanin Rasha da Ukraine

January 4, 2006

An cimma daidaituwa akan rikicin gas tsakanin Rasha da Ukraine

https://p.dw.com/p/Bu2k

Bisa ga ra’ayin Cornelia Rabitz dai wannan daidaituwar da aka cimma abu ne da ya kamata ya samu tun da dadewa. Bayan kashe dare da suka yi suna famar kai ruwa rana wakilan kasashen Rasha da Ukraine, a yau da sanyin safiya sun ba da sanarwa akan dinke barakar da ta samu tsakanin kasashen biyu akan cinikinsu na gas. Sakamakon taron nasu kuwa yana da sarkakiyar gaske. Daidaituwar da aka cimma a takaice ita ce, ita Rasha, kamar yadda aka shirya tun farko zata daga farashin gas din zuwa dala 230, a yayinda ita kuma Ukraine ke da cikakken ikon sayen gas daga kasashen tsakiyar Asiya akan farashi mai rahusa. Sannan a daya hannun kasar zata yi karin ladar da take karba daga Rasha dangane da amfani da harabarta da take yi wajen shigar da gas dinta zuwa kasashen yammacin Turai. Duk dai wanda yayi bitar wannan daidaituwa da aka cimma zai ga cewar ba wanda aka kwara, kowane bangare na da ikon ikirarin samun galaba akan dan-uwansa. Bugu da kari kuma wannan daidaituwa zata taimaka a kauce wa wani mummunan bala’i na karancin makamashi a kasar Ukraine da sauran kasashen Turai. Abin takaici a nan shi ne rashin hangen nesa da sassan suka kasa yi tun da farko. Duk kuma da wannan ci gaba da aka samu za a ci gaba da tuhumar fadar mulki ta Kremlin da kokarin amfani da albarkatun kasar da Allah Ya fuwace wa Rasha domin cimma bukatunta na siyasa. Ita kuma kasar Ukraine, wannan rikici ya zama tamkar darasi gare ta domin ta gane cewar bin manufofi na sakarwa da harkokin kasuwanci mara ba abu ne mai sauki ba. Ka da ta taba tunanin cewar zata samu wani rangwame ko wata gata da tsofuwar kawarta Rasha. Mai yiwuwa ita Rashan ta nemi yin amfani da wannan dama ne domin yin tasiri a siyasar Ukraine ta la’akari da zaben da ake shirin gudanarwa a kasar nan da watanni uku masu zuwa. Mi yiwuwa niyyarta ce ta kara zubar da martabar gwamnatin shugaba Yuschtchenko a idanun jama’a ta yadda magoya bayan manufofin Rasha zasu samu ci gaba lokacin zaben. Amma fadar mulki ta Kremlin bata samu biyan bukata ba daidai da yadda murnarta ta koma ciki lokacin da tayi kokarin yin shisshigi a zaben shugaban kasar Ukraine da aka gudanar a shekara ta 2004. Maganar kudi dai ga alamu ita ce ta taka muhimmiyar rawa a zauren shawarwarin. Domin kuwa samun karancin yawan gas da Rasha ke sayarwa ga kasashen yammacin Turai na ma’anar raguwar yawan kudadenta na shiga. Kuma ga alamu ganin yadda kasashen suka fara batu a game da wata hanya dabam da samun makamashi, shi ne ya sanya kamfanin gasprom na kasar Rasha ya ba da kai bori ya hau domin cimma daidaituwa a cikin gaggawa.