1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Chadi sun halaka ´yan tawaye 300 a kan iyakarta da Sudan

December 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvFh

Jami´an kasar Chadi sun ce dakarun gwamnati sun kashe mutane sama da 300 a matakan da suka dauka na murkushe wani harin ´yan tawaye a garin Adre dake kan iyakar Chadi da Sudan. A cikin wata sanarwa da ya bayar, ministan harkokin wajen Chadi Ahmat Allam-Mi ya ce an fatattaki sauran ´yan tawayen har zuwa wani yankin kan tsaunuka dake cikin Sudan. To sai dai majiyoyin gwamnati sun ce har yanzu ana ci-gaba da daukar matakan soji a yankin da ke ciki da wajen garin Adre mai nisan kilomita kimanin dubu daya gabas da N´djamena babban birnin kasar.