1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun gwamnatin Sudan sun ƙaddamar da sabin hare-hare a Darfur

October 9, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8t

Rundunar gwamnatin ƙasar Sudan, tare da tallafin mayaƙan Janjawid,ta ƙaddamar da wasu sabin hare-hare a yankin Darfur.

Rahotani daga wannan yanki sun ce runduna ta abkwa garin Mouhadjiriya, dake kudancin Darfur.

Wannan gari na cikin kullar ƙungiyar tawaye ta SLA, ƙungiya ɗaya tilo, da ta rattana hannu, akan yarjejeniyar zaman lahia, da gwamnatin Khartum.

Shugaban ƙungiyar SLA, Mohamed Bashir, ya sanar manema labarai cewar, wannan hari ya kawo ƙarshen yarjeniya da su ka cimma da gwamnati, kuma a yanzu, dakarun SLA, za su shiga yaƙi da gwamnatin bil haƙi ada gaskiya.

A cewar shugaban na SLA, a ƙalla mutane 105, su ka rasa rayuka a cikin wannan saban hari.

Saidai ya zuwa yanzu, gwamnatin Sudan, da ƙungiyar taraya Afrika, basu ce komai ba, a game da wannan labari.

Cemma dai, idan ba a manta ba, a makon da ya gabata dakarun gwamnatin Sudan sun kai hari a garin Haskinita, wanda su ka aske kwata-kwata.