1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

dakarun gwamnatin Uganda sun fara janyewa daga arewacin ƙasar

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bul8

Gwamnatin Uganda ta bayyana janye dakarun ta daga arewancin ƙasar, kwana ɗaya bayan fara aiki da yarjejeniyar zaman lahia da ta cimma, tare da yan tawayen LRA.

Saidai kakakin rundunar gwamnati da ya bayyana labarin bai faɗi yawan sojojin da su ka janye ba.

Al´umomin Uganda, mussamman na yankunnan da rikicin ya shafa, sun shirya tafiyar jerin gwano cikin lumana, domin nuna farin ciki ,a game da massalaha da aka samu a cikin wannan rikici da ya ɗauki tsawan shekaru kussan 20 a na gwabzawa.