1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Habasha sun shiga birnin Mogadishu

Hauwa Abubakar AjejeDecember 28, 2006

Dakarun gwamnatin Somalia da goyon bayan dakarun Habasha sun shiga cikin birnin Mogadishu ba tare da wata adawa ba, bayan shugabanin kotunan islama suka tsere daga birnin Mogadishu

https://p.dw.com/p/Btwr
Hoto: AP

Firaministan Somalia Ali Muhammad Gedi ya sanarda manema labarai jim kadan bayan iasarasa wajen birnin na Mogadishu cewa tuni sun shiga cikin wasu bangarori na Mogadishun.

Ya isa ne tare da minister Hussein Aidid da komishinan yan sanda Ali madobe dukanisnu tsoffin madugan yaki da dakarun islama suka kora birnin Mogadishu.

Ali Gedi ya isa garin Afgoye kilomita 20 daga Mogadishu saoi kadan bayan ficewar shugabanin kotunan islama daga birnin.

Ya kuma tattauna da shugabanin kabilun yankin da kungiyoyi don tattauna yadda zaa kima birnin zuwa hannun dakarun gwamnati.

Gedi yace tattaunawar tasu bata hada da shugabanin kotunan musuluncin ba.

Su dai shugabanin kotunan islama sun kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a birnin Mogadishu suna masu kafa shariar musulunci,bayan korar madugan yaki da suke samun goyon bayan Amurka.

Yanzu dai haka mazauna birnin sunce babu doka da oda bayan ficewar shugabanin kotunan musuluncin daga birnin,inda ya koma yadda yake a da,cikin rudani da tashin hankali.

A nashi bangare dai firaministan Habasha Meles zenawi ya fadawa manema labarai a birnin Addis Ababa cewa dakarunsa zasu bi shugabannin kotunan islaman ko ina suka shiga,yana mai cewa suna tattauna hanyoyi da zasu bi na ganin cewa birnin Mogadishu bai fada wani mummunan hali ba.

Zenawi yace dakarunsa sun kashe akalla mayakan islama 2,000 zuwa 3,000 tare da yiwa dubbai kuma rauni.

Shugabannin sun dauki wannan yaki tsakaninsune da Habasha ba gwamnatin Somalia ba,sai dai jakadan Amurka na wucin gadi a MDD Alejendro Wolff yace kuskure ne a ce dakarun Habasha suka haddasa rikicin na Somalia.

“kuskure ne a dauki wannan batu da kuma matsalar a sakamakon dakarun Habasha a kasar.akwai batutuwa da dama daya kamata bangarorin Somalia su magance su,wato gwamnatin kasar da kuma kotunan muslunci.

Kakakin gwamnati Abdurahman Dinari yace tuni dakarunsu sun kame muhimman wurare na birnin,ya kuma fadawa gidan TV na Aljazeera cewa gwamnatin ta kafa dokar tabaci domin maido da doka da oda a cikin birnin.

Sai dai kuma shugaban kotunan musuluncin yace janyewarsu daga birnin Mogadishu wata dabara ce a wannan yaki da aka fara mako guda daya wuce tsakanisnu da dakarun Habasha dake goyon gwamnatin rikon kwarya mai rauni a kasar ta Somalia.

Sheikh Ahmed yace sun janye ne domin rage zubda jini tare da kare abinda ya abku lokacinda aka fatattaki dakarun Amurka daga Mogadishu shekaru 10 da suka shige.

Sakatare janar mai barin gado na MDD Kofi Annan yace bai dace ba a wannan lokaci kasashe makwabta su shiga cikin rikicin na Somalia.

“ina rokon kasashe makwabta da su janye daga sa kansu cikin wannan rikici na Somalia su kuma mutunta kasancewar kasar mai yancin kanta”

Gwamnatin ta wucin gadi dai tayi tayin ahuwa ga dukkan mayakan islama wadanda suka ajiye makamansu.