1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Iraki sun kashe mayakan kungiyar IS 2500 a Falluja

Mohammad Nasiru AwalJune 20, 2016

Yanzu haka sansanonin 'yan gudu hijira a Iraki sun cika makil da mutane da suka tsere daga yakin na Falluja.

https://p.dw.com/p/1JAGn
Irak Kämpfe um Falludscha
Hoto: Reuters/T. Al-Sudani

Dakarun kundunbala na Iraki da ke karkashin hukumar yaki da ta'addanci suna dab da kawo karshen matakan sojin da suka dauka da nufin fatattakar mayakan kungiyar IS daga birnin Falluja. Kwanaki kalilan da suka gabata dakarun Irakin sun karbe iko da tsakiyar birnin na Falluja sannan suna tono nakiyoyin karkashin kasa da sauran bama-bamai da mayakan IS suka bari. Kwamandan dakarun yaki da ta'addanci Janar Abdul Wahab Aisaidi ya fada wa kamfanin dillancin labarun Reuters yadda dakarunsa suka ci lagon mayakan IS, suka kuma kwace iko da tsakiyar birnin.

Ya ce: "Akwai mayaka kusan 2000 a kan tituna da wasu 1000 zuwa 1500 a cikin gidaje da suka shiga fafatawar, amma mun kashe fiye da 1500, sannan wasu dakarun tsaron sun kashe fiye da 1000. Wato abin nufi abokan gaba sun yi asarar mutum fiye da 2500, kuma mun tsare wasu 1000, wasu kadan kuma sun tsere."

Yanzu haka sansanonin 'yan gudu hijira a Iraki sun cika makil da mutane da suka tsere daga Falluja.