1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Isra’ila sun kutsa cikin Zirin Gaza a daren jiya.

June 28, 2006
https://p.dw.com/p/BusP

Hukuimar rundunar sojin Isra’ila ta tabbatad da kutsawar dakarun ƙasar bani Yahudun cikin zirin Gaza a daren jiya, a wani yunƙuri na ceto wani sojan ƙasar da ’yan ta kifen Falasɗinawa suka yi garkuwa da shi tun ran lahadin da ta wuce. Isra’ila ta fara ɗaukin ne da tankunan yaƙi da kuma jiragen sama masu saukar ungulu, tare da kai hare-haren sama kan wasu gadoji 3 da kuma tashar samad da wutar lantarki a Zirin Gazan. Rahotannin sun ce babu wutar lantarki yanzu a yankin gaba ɗaya. Kawo yanzu dai, ba mu sammi rahotannin asarar rayuka ba, amma maneman labarai sun ruwaito cewa, an yi ta jin ammon bindiga a sassa daban-daban. Wasu rahotannin kuma sun ce, iyalan Falasɗinawa da yawa sun ƙaurace zuwa garin Rafa, da ke iyaka da Masar, yayin da ’yan ta kife kuma suka yi ta datse hanyoyi. Wasu ’yan rukunin Falasɗinawan da ya yi garkuwa da sojan Isra’ilan, sun yi barazanar kashe shi, idan mahukuntan ƙasar ba su sako matan Falasɗinawa da yara ƙanana da suka tsare a kurkuku ba. Tun da Isra’ilan ta janye daga zirin Gaza a shekarar bara dai, ba a taɓa samun hauhawar tsamari mafi muni tsakanin ɓangarorin biyu kamar wannan karon ba.