1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai na cikin shirin ko ta kwana a ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango.

November 17, 2006
https://p.dw.com/p/Buba

Dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya, sun yi ta sintiri a Kinshasa, babban birnin ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, sakamakon hauhawar tsamarin da aka samu, bayan an ba da sanarwar cewa shugaba mai ci yanzu, Joseph Kabila ne ya lashe zaɓen zagaye na biyu na shugaban ƙasar, da aka gudanar a ran 29 ga watan Oktoba.

An tura dakarun na ƙasa da ƙasa su yi ta sintiri ne a yankuna daban-daban na ƙasar, don hana sake aukuwar fafatawar da ta ɓarke tsakanin sojoji da magoya bayan ’yan takaran biyu a zaɓen, wato shugaba Joseph Kabila da abokin hamayyarsa, Jean-Pierre Bemba, a birnin Kinshasa a makon da ya gabata. Shi dai Bemba ya ce yana watsi da sakamakon zaɓen, kuma zai ƙalubalance shi ne ta hanyar doka.