1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Siriya sun kwace daukacin Palmyra

Ahmed SalisuMarch 28, 2016

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya jinjinawa dakarun Siriya bayan da suka karbe iko da garin Palmyra daga hannun mayakan kungiyar IS da ke rajin girka daular Islama.

https://p.dw.com/p/1IKoS
Syrien Palmyra UNESCO Weltkulturerbe - Rückeroberung durch syrische Armee
Hoto: Getty Images/AFP/M. Al Mounes

Rashan har wa yau ta taya Siriya murna dangane da wannan nasara da ta samu ta kakkabe 'yan kungiyar ta IS daga garin bayan da suka shafe tsawon loakci su na rike da shi.

Shugaban Siriya din Bashar al-Assad ya ce wannan nasarar da aka samu a Lahadin da ta gabata aba ce da ke da muhimmancin gaske a yakin da hukumomin Siriya din ke yi da 'yan kungiyar ta IS.

Yanzu haka dai kwararru za su duba irin halin da birnin ke ciki musamman ma dai kayan tarihin da aka lalata lokacin da 'yan IS din ke rike da Palmyra.

Wani dan jarida na kamfannin dillancin labarai na AFP da ya garin ya ce an yi ta'adi matuka gaya domin kuwa wajen ya kasance kamar kufayi.

Yanzu haka dai al'ummar kasar ta Siriya na ta bayyana gamsuwar bisa wannan nasarar da aka samu inda suke fatan ganin haka a wasu sassan kasar da ke hannun 'yan IS.