1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

dakarun Sri Lanka sun kashe ´yan tawayen Tamil Tigers 150 a garin Mutur

August 5, 2006
https://p.dw.com/p/Buni
Dakarun Sri Lanka sun ce sun sake kwace ikon garin Mutur dake gabar tekun gabashin kasar bayan wani kazamin fada da suka fafata da ´yan tawayen Tamil Tigers, wadanda suka farma garin a ranar laraba da ta gabata. Ma´aikatar tsaro a birnin Colombo ta ce dakarunta sun halaka akalla ´yan tawaye 150 a wannan yanki. Ma´aikatan agaji sun ce fiye da mutane dubu 20 suka makale a garin na Mutur sakamakon wannan fada. Fadan na baya bayan nan dai shi ne mafi muni tun bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a shekara ta 2002. To amma duk da haka gwamnatin Sri Lanka ta dage kan cewa tana aiki da ka´idojin yarjejeniyar dakatar da yakin.