1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakatar da shugaban izraela daga mulki

Zainab A MohammadOctober 29, 2006
https://p.dw.com/p/Bu56

Rahotanni kafofin yada labarun Izraela na nuni dacewa,anasaran babban Alkalin kasar Menachem Mazuz,zai bukaci Shugaba Moshe Katsav daya dakatar da kanshi daga kujerar shugabancin Izraelan ,sakamakon samunshi da da laifin yin fyade da yansanda sukayi.Rahotanni sunyi nuni dacewa Alkali Muzuz zai gabatar da wannan bukatu ne ,a matsayin martani kann takartan zargi da babban kotun kasar ya gabatar akan Mr Katsav mai shekaru 60 da haihuwa,wanda kuma ya karyata zargin fyade da ake masa.A ranar 15 ga watan oktoban daya gabata nedai maaikatar Sharia da yansandan Izraelan suka gabatar da sanarwar hadion gwiwa dake nuni dacewa ,sun samu shaidu gamsassau dake dangana Shugaba Katsav da laifuffukan Fyade ,na tilas akan maaikata mata ba tare da amincewarsu ba .Yanzu dai ya ragewa babban mai shariar kasar na daukan matakin tsige shugaban kasar.

Rahotanni daga Izraelan na nuni dacewa,Umurnin Kotun zai bukaci Mr Katsav,daya dakatar da gudanar da aiki a matsayin shugaban kasa,domin bawa kotu daman gudanar da shariar ,domin maaikata da dama sunki bada shaida akansa.