1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakile kaifin kishin addini a Turai

Gazali Abdou TassawaAugust 23, 2016

Gwamnatocin kasashen Turai na yin nazarin kan hanyoyin yaki da tsautsauran ra'ayin addini da ke ci gaba da yaduwa a cikin kasashen na Turai.

https://p.dw.com/p/1Jngt
Belgien Sicherheitskontrolle am Hauptbahnhof in Brüssel
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Gambarini

Shugaban Faransa Francois Hollande da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma firaministan Italiya Matteo Ranzi sun hadu domin tattaunawa kan kalubalan da Turai ke fuskanta wanda suka hada da hare-hare ta'addanci da kwararowar 'yan gudun hijira da kuma ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai. Kazalika wadannan magabata uku za su tsara taron kolin na kasashen Turai da zai gudana a ranar 16 ga watan Satumba.

Italien Dreiergipfel zwischen Merkel, Holland und Renzi
Hollande da Merkel da Renzi na kokari wajen dakile ta'addanci a TuraiHoto: Reuters/R. Casilli

Daya daga cikin muhimman batutuwan da taron kolin zai mayar da hankali a kai shi ne na yaduwar tsatsauran ra'ayin addinin Islama a cikin kasa. Yanzu haka kungiyoyin kasar Jamus da dama ne suka dukufa kan nazarin wadannan matsaloli. Thomas Mücke daya daga cikin shugabannin kungiyar rigakafin afkuwar tashe-tashen hankula ta Violence Prevention Network na ganin makarantun boko na daga cikin muhimman wuraren da ya kamata a dauki irin wadannan matakai na rigakafi.

A hannu guda kuma Thomas Mücke ya ce akwai hanyoyi da dama na sauyawa mutum mai tsatsauran ra'ayi tunaninsa inda ya ce a wannan fannin Jamus ta cimma nasarori da dama har ma ya ce ''yankuna da dama sun kaddamar da tsari na kyautata rayuwar matasa da samar masu da aikin yi da ma fadakar da su, ko da ya ke mutanen da ke halartar irin wadannan cibiyoyin sun fara yin yawa".