1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNajeriya

Dalibai sun samu izinin ciyo bashin kudin makaranta

Uwais Abubakar Idris
April 4, 2024

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar samar da bashi ga daliban da ke karatu a jami'o'in Najeriya domin tallafa wa marasa karfi.

https://p.dw.com/p/4eQoh
Hoto: Sunday Aghaeze/AP Photo/picture alliance

Wannan doka da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya rattabawa hannun ta sake farfado da tsarin ba wa daliban jami'o'i bashin kudi ne don su samu karatun boko a manyan makarantu.

A bisa tsarin za'a bai wa kowane dalibi da ya cancanta bashin da ba kudin ruwa a ciki na Naira dubu 500 a kowace shekara har tsawo shekaru hudu na karatunsa. Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana manufarsa jim kadan bayan rattaba hannu a kan sabuwar dokar yana mai cewa

karin bayani : Takaddama a Najeriya a kan Shaidar digiri daga Togo da Benin

‘'A yanzu muka sanya hannu kan dokar fara aiki da bada bashi ga dalibai, babu wani wanda duk tsanain talaucinsa za a hana shi damar samun ingantaccen ilimi a Najeriya, muna a wannan matsayin ne saboda dukkanmu muna da ilimin kuma an taimaka mana, kuma akwai tsarin yadda dalibai za su karbi wannan bashin muddin dai kai dan Najeriya ne.''

Nigeria Bildung l Universität Lagos l Streik der Universitätsdozenten
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture-alliance

Karin bayani : Dawo da koyar da tarihi a manhajar karatu a Najeriya

Murna da da doki ya mamaye zukatan daliban Najeriya, bayan da batun bada bashi don a yi karatun boko ya yi masu nisa, kana hukumar kula da bada bashi ga dalibai ta Najeriya ta tsara cewa daliban da za su ci amfanin bashin za su biya ne a lokacin da suka kama aiki inda za'a rinka cire masu kaso 10 daga cikin albashinsu har su biya, kuma za su iya kara yawan abinda za su biya har zuwa kashi 100. 

Karin bayani :Tsadar kudin makaranta na addabar dalibai a Najeriya

Sake farfado da tsarin bai wa daliban jami'oi bashi a Najeriya na da muhimmanci musamman a daidai wannan lokaci da tsadar rayuwa ke sanya daliban da iyayensu ba su da halli gaza kamala karatunsu a kasar.