1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalilan 'yan Iritiriya na gudun kasarsu

Usman Shehu Usman/ UAApril 15, 2016

'Yan Iritiriya na tserewa daga kasarsu bisa dalilai na cin zarafi daga gwamnati. Sun kasance a sahu na bakwai na kasashe da ke da yawan 'yan gudun hijira a Jamus.

https://p.dw.com/p/1IWW6
Eritrea - Bilder Übernahme DLF-Artikel
Hoto: Deutschlandradio/Oliver Ramme

Dalilan 'yan Iritiriya na tserewa daga kasarsu

Gwamnatin Iritiriya bata taba yin zabe ba tun bayan samun 'yancin kai shekaru 23 da suka gabata. Sannan kafafen yada labarai duk suna karkashin gwamnati, Akwai dubban fursunoni da ke daure a gidan yari ba tare da yi musu shari'a ba. Hatta masu karfi a jika na kasar ba su da duk wani 'yanci na rayuwa. Wadanda ke rayuwa karkara sun ma fi samun walwala duk cewa akwai matsalar kwararar hamada, kamar yadda Tesfalem Andom mai garin kauye Tokombia da ke iyaka da kasar Habasha ke cewa.

"Anan muna matukar samun daukacin 'yancin rayuwa. A kan iyakar komai lafiya ba tashin hankali. Bamu cika samun wata matsala ba. Kuma bama son samun sabani da kasar Habasha"

Eritrea Flüchtlingslager in der Region Tigrai Äthiopien
'Yan Iritiriya na gudun hijira a kasashe da ´damaHoto: Reuters/T. Negeri

Gwamnati na tilasta wa 'yan Iritiriya yin bautar kasa

A Kasar ta Iritiriya ba wani cikakken kundin tsarin mulki balle batun demokuradiyya. Amma akwai dokar cewa dole duk wanda ya kai shekaru 18 yayi aikin bautar kasa. Ana tilasta yin bautar kasar walau a kamfanoni ko a hukumomin tsaron kamar na soji inda ake koya wa mutane sabar bindiga, wannan bautar kasar na daya daga abin da ke sa akasarin yan Iritiriya gudu daga kasarsu. Sai dai mai garin na Tokombiya ya ce bai ga wata matsala ba a lamarin.

"Wannan ai haka rayuwa ta gada: wasu su tafi wasu su shigo: Suna tafiya gun-gungu i zuwa kasar Habasha, in sun je su kan ji ba dadi, anan tattarasu a sansanin 'yan gudun hijira. Tserewa daga kasa ya na neman zama wani sabon yayi da matasa ke son yi"

John wanda ke da zama a Asmara babban birnin kasar ya ki bayyanan asalin sunansa, hatta muryasa ya nemi da a surka, domin ga duk mai sukar gwamnati to anan iya daureshi a kurkuku ba tare da samun lawya ba. Kuma babu wanda ya san irin tara da za iya masa.

Eritrea Kinder im Flüchtlingslager in der Region Tigrai Äthiopien
Yara na cikin mawuyacin hali a IritiriyaHoto: Reuters/T. Negeri

"Ba ni da kwarin gwiwar yin aiki wanda ba'a biyan albashi. Ina matukar son ganin na yi wani aiki inda zan koyi wata sana'ar, sai dai kuma dole in nemi aikin da zan samu kudin kula da rayuwata"

A Kasar ta Iritiriya dai, wasu kungiyoyi sun fara kafa san'a'io da kuma horoas da matasa don dogaro da kai. Sai dai ko da matasan sun koyi aiki babu inda za su yi aikin. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa 'yan kasar ta Iritiriya ke son yin hijira ba tare da damuwa da irin hatsarin da ke kan hanyar shiga Turai ba.