1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dalilin murabus na Köhler

May 31, 2010

Shugaban Jamus, Horst Köhler ya yi murabus ba tare da wani jinkiri ba

https://p.dw.com/p/Ne51
Horst KöhlerHoto: AP

Shugaban kasa na Jamus, Horst Köhler ranar Litinin ya sanar da cewar ya yi murabus daga mukaminsa. Lokacin bayanin haka gaban  manema labarai, tsohon shugaban na Jamus ya ce ya yi haka ne saboda abin da ya kira, rashin baiwa ofishin shugaban kasa daraja da mutuncin da ya dace a kasar ta Jamus. Köhler shi ne shugaban Jamus na farko da ya sauka daga mukaminsa, tun  kafin karshen wa'adin da aka zabe.

Tun kafin shugaban na Jamus ya dauki wannan mataki na murabus daga mukaminsa,  sai da akai ta sukan sa sakamakon wani jawabi da ya yi lokacin hira da wata tashar rediyo, inda ya nuna alamun  goyon bayan amfani da karfin soja, domin kare manufofin Jamus, musamman a fannin ciniki.

Tun da farko sai da shugaban ya gaiyaci yan jarida zuwa fadarsa a Berlin da ake kira Schloss Bellevue ba tare da ya nunar da dalilin wannan gaiyata ta gaggawa ba, ko da shike ganin yadda ya baiyana tare da mai-dakinsa, ya sanya yan jaridan suka fara gane cewar duk abin da zai fadi, zai girgiza al'amuran siyasa a nan Jamus. Wannan zato nasu kuwa ya tabbata gaskiya, domin kuwa   tsohon shugaban kasar ya fara da cewa:

Ina  tabbatar da murabus dina daga mukamin shugaban kasa na Tarayyar Jamus, ba tare da wani jinkiri ba. Ina mika godiya ga  dimbin mutane da suka nuna amincewar su gareni, suka kuma nuna goyon bayansu ga ayyukan da na tafiyar. Ina rokon su fahimci dalilan da suka sanya na dauki wannan mataki.

Horst Köhler,  ya yi wa  manema labaran bayani dalilan da suka sanya  ya yi murabus daga mukaminsa, inda ya ce hakan yana tattare ne da sukan da ake ta masa, sakamakon jawaban da ya yi game da ayyukan sojojin rundunar Jamus, wato Bundeswehr.   Ranar 22 ga watan Mayu, lokacin hira da wata tashar rediyo, Köhler ya ce kasa  kamar Jamus da ta dogara ga ciniki da kasashen ketare tilas ne ta fahimci cewar idan bukata ta taso,  ta yi amfani da karfin soja domin kare bukatun ta, alal misali, hanyoyin da take bi wajen ciniki.

Horst Köhler und Umar Musa Yar'adua
Köhler da marigayi Yar'aduaHoto: picture-alliance / dpa / AP / DW Montage

Ya ce wadannan jawabai da nayi a game da aiyukan rundunar ta Jamus, sun fuskanci suka mai tsanani. Ina bakin cikin ganin wadannan jawabai nawa  kan wannan al'amari mai wahala da muhimanci ga kasar mu, an kasa fahimtar su. Wadannan soke-soke sun kai matsayin da har ma aka zarge ni da laifin goyon bayan  aiyukan sojojin na Jamus da ba su dace da  tsarin mulkin kasar mu ba. Wannan zargi ko kadan babu  gaskiya a cikin sa. Hakan ya shigar da rashin darajantawa da mutunta ofishi na.

Tsohon shugaban kasa, Horst Köhler yace  tun da farko sai da ya sanarwa da wannan kudiri nashi ga shugaban gwamnati, Angela Merkel da mataimakin ta, Guido Westerwelle da  wanda zai rike aiyukan shugaban kasa har kafin a zabi sabo,  da shugaban  kotun kare tsarin mulki na taraiya. Ministan harkokin waje, Guido Westerwelle  ya baiyana bakin cikin murabus  na Köhler inda yace:

Shugaban kasa ya sanar dani  da rana game da  kudirin sa na murabus. Lokacin   magana dashi, nayi kokarin jan hankalinsa kada ya sauka. To amma yace haka ya zaba. Ina bakin cikin  daukar wannan mataki da yayi, kuma ina mutunta matakin. Na godewa shugaban na taraiya saboda  gagarumin aikin da yayi wa al'ummar mu  tun daga   shekarun baya.

A karshen jawabin sa,  tsohon shugaba Köhler yace abin alfahari ne a gareshi,  yayi wa  Jamus aiki a matsayin shugaban kasa.

Ga wasu ra'ayoyin masu sauraro:

Ahmed Garba Idris, Sokoto/Nigeria:

To shugabannin Afirka ya kamata ku yi koyi da shugaban kasar Jamus domin yau an wayi gari ya yi murabus saboda wasu akidu na gwamnati da ba su yi dai dai da akidunsa ba.

Salisu Shehu, Kano/Nigeria:

A dai dai lokacin da shugabannin kasashen Afirka musamman Nigeria ke kokarin dauwama a kan mulki ko da talakawa ba sa so duk kuwa da zaluncin da suke yi, yau ga shugaban kasar Jamus ya yi murabus saboda ba a tafiyar da tsarin gwamnati yadda ya kamata duk kuwa da cewa talakawa sun shaida ana kwatanta adalci.

Aminu Mai shayi Garba Cede, Taraba/Nigeria:

Allah ya sa murabus din shugaban kasar Jamus ba zai kawo koma baya a dangantakar Jamus da kasashen Afirka ba.

Ibrahim Bena Hashidu, Nigeria:

Murabus din Shugaban Kasar Jamus babban koma baya ne ga nahiyar Afirka.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Abdullahi Tanko Bala