1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar siyasa a ƙasar Italiya

April 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2E

Shugaban jamíya mai sassaucin raáyi a ƙasar Italiya Romano Prodi, ya dage a kan nasarar da yace jamíyar sa ta samu a zaɓen majalisun dokoki, duk da ƙin amincewar P/M Silvio Berlusconi ya sauka daga muƙamin sa, inda yake daáwar an tafka magudi. Berlusconi yace ba za su amince da sakamakon zaɓen ba, har sai an bada hukunci sahihi a kan sakamakon, a saboda haka yace babu wanda zai ikirarin cewa shi ne ya lashe zaɓe. Yana mai cewa ba ya fidda tsammanin soke sakamakon ƙuriún da yan Italiyan mazauna ƙasashen ƙetare suka kaɗa, na kujeru shida na majalisun dokoki, wanda yace yana cike da maguɗi. Berlusconi ya bada shawarar ɗaukar darasi daga tsarin siyasar Jamus na kulla kawance a tsakanin jamíyun idan aka yi kunnen doki a zagaye na biyu na zaɓen. A ƙarƙashin tsarin ƙasar Italiya, dukkanin majalisun dokokin biyu, na wakilai dana dattijai na da karfin iko daidai wa daida, abin da kuma ke nufin cewa wajibi ne a sami jituwa domin gudanar da gwamnati yadda ya kamata.