1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar siyasa a fadar White House ta Amirka

October 29, 2005
https://p.dw.com/p/BvNR

Shugaban Amirka GWB na kokarin kwantar da hankalin jama´a bayan wani rikicin siyasa na cikin gida da ya kunno kai sakamakon murabus din da Lewis Libby babban mai bawa mataimakin shugaban Amirka shawara ya yi. A lokacin da yake magana a birnin Washington shugaba Bush ya ce ko da yake an dukufa a binciken da ake yi, to amma fadar White House ba zata yarda a jefa ta cikin wani mawuyacin hali ba. Bush ya kara da cewa har yanzu zato ake yi cewa Libby ya aikata wani laifi. A jiya juma´a Libby mai bawa mataimakin shugaban Amirka Dick Cheney shawara ya ajiye aikinsa jim kadan bayan tuhumarsa da hana shari´a ta yi aiki da rantsuwa kan karya da kuma fadi ba daidai ba. Wannan tuhumar dai na da alaka da binciken da ake yi na bayyana asali ko kuma sunan wata jami´ar hukumar leken asirin Amirka CIA wato Valerie Plame a lokacin bazarar shekara ta 2003. Masharhanta na Amirka sun ce an tona asirin matar ce a matsayin ramuwar gayya da adawar da mijinta ya nuna wa yakin da Amirka ta kaddamar akan Iraqi.