1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

200709 Honduras Staatskrise

July 20, 2009

Bayan kwanaki biyu ana tattaunawa mai tsauri tawagogin sojin da suka yi juyin mulki da na shugaban ƙasar da aka hamɓarar sun bayyana cewa tattaunawar ba ta yi nasara ba

https://p.dw.com/p/ItCE
Tawagogin taron sulhun Honduras da shugaban Costa Rica Oscar Arias a tsakiyaHoto: AP

Kimanin makonni uku da suka gabata sojoji a ƙasar Honduras suka hamɓarar da shugaba Manuel Zelaya wanda aka zaɓa ta hanyar ɗemokuraɗiyya. Jim kaɗan bayan haka aka fara tattaunawa tsakanin wakilan sabuwar gwamnati da na hamɓararren shugaba Manuel Zelaya a ƙasar Costa Rica ƙarƙashin jagorancin shugaban Costa Rica Oscar Arias. To amma tattaunawar ta wargaje a jiya Lahadi dangane da batun ko Zelaya zai iya komawa kan muƙaminsa ko a´a.

Bayan kwanaki biyu ana tattaunawa mai tsauri tawagogin gwamnatin da ta yi juyin mulki da na shugaban ƙasar da aka hamɓarar sun bayyana gaban ´yan jarida suna masu cewa tattaunawar ba ta yi nasara ba. Babban mai shiga tsakanin kuma shugaban ƙasar Costa Rica Oscar Arias ya nuna matukar rashin jin daɗinsa da wannan tsaikon da aka samu.

Ya ce: "Shin muna da zaɓi da ya fi tattaunawa da juna? Al´umar Honduras suna da makami kuma sun san da haka. Mai zai faru idan aka yi setin wannan makami akan ani soji? Ko kuma idan wani soji ya harbi farar hula? Hakan ka iya haddasa yaƙin basasa wanda ko kaɗan bai kamata ya faru a Honduras ba."

Arias ya ba gabata da jerin shawarwari bakwai waɗanda suka tanadi kafa wata gwamnatin haɗin kan ƙasa da sasantawa ƙarƙashin shugabancin Manuel Zelaya bisa sharaɗin cewa zai yi watsi da aniyarsa na canza kundin tsarin mulkin ƙasa, abin da ya janyo faɗuwarsa makonni uku da suka wuce.

Bisa shawarar ta shugaba Arias ana iya yiwa sojojin da suka yi juyin mulkin afuwa wadda haka za ta ba da damar shigar da su cikin gwamnatin haɗin kan ƙasa. Sannan Arias ya so a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da aka shirya yi cikin watan Nawumba, makonni huɗu gaba da wa´adi, sannan wata hukumar ƙasa da ƙasa ta sa ido kan komawa ga bin dokokin kundin tsarin mulkin ƙasar. Tawagar Zelaya dai ta amince da waɗannan shawarwarin amma abokiyar tattaunawar ta yi watsi da su kamar yadda wakilinta Carlos Lopez ya nunar.

Ya ce: "Ka yi mana gafara shugaba Arias, domin shawarwarin da ka gabatar mana ba abin karɓuwa ba ne ga halattaciyar gwamnatinmu ta Honduras. Musamman ba za mu iya amincewa da rukunin farko na shawarwarin ba."

Shawarar farko dai ta tanadi komawar Zelaya kan muƙamin shugaban ƙasa. Yanzu dai ba a sani ba ko za a ci-gaba da tattaunawar a ƙasar Costa Rica. Ko da yake a halin da ake ciki wakilan tawagar Zelaya sun ce an kawo ƙarshen wannan tattaunawa saboda taurin kai na ɗaya ɓangaren to amma sun ci gaba da cewa har yanzu ƙofofinsu na shawarwari a buɗe suke ga Arias a natsayin mai shiga tsakani. Su ma sojojin da suka yi juyin mulkin sun nuna aniyar gudanar da shawarwarin. A cikin sa´o´i 72 masu zuwa Arias zai fara wani sabon yunƙurin shiga tsakani.

To sai dai har yanzu ana cikin wani hali mai hatsari domin idan Zelaya ya ci-gaba da dagewa kan komawa kan mulki sannan su kuma sojoji suka ƙi to kenan babu sauran damar tattaunawa. Yayin da har yanzu ake ci-gaba da zanga-zangar nuna adawa da juyin mulkin a Honduras shi kuma Zelaya ya ce a wannan makon zai koma ƙasar ko an yi sulhu ko ba a yi ba.

Mawallafa: Anne-Kathrin Mellmann/Mohammad Awal

Edita: Zainab Mohammed