1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambe: Mayweather ya doke McGregor

Gazali Abdou Tasawa
August 27, 2017

Shahararren dan damben zamani nan dan kasar Amirka Floyd Mayweather ya doke Conor McGregor dan kasar Aylan a karawar da suka yi a daren Asabar washe garin wannan lahadi a birnin Las Vegas a gaban 'yan kallo dubu 20.

https://p.dw.com/p/2iuVL
USA Las Vegas Boxkampf Floyd Mayweather Jr. -  Conor McGregor
Hoto: Reuters/S. Marcus

Shahararren dan danben zamani nan dan kasar Amirka Floyd Mayweather ya bige Conor McGregor dan kasar Aylan a karawar da suka yi a birnin Las Vegas na jihar Nevada a gaban 'yan kallo dubu 20 da wasu miliyan dubu a gaban akwatinan Talabijin. Alkali ya tsaida damben ne a zagaye na 10 bayan da McGregor ya kusa ya fita hayyacinsa a sakamakon jerin naushin da ya sha a fuska da ta kai ga kumbirewa.