1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwar AU a game da shirin zaɓe a Cote d´Ivoire

May 30, 2006
https://p.dw.com/p/BuwC

Ƙungiyar Gamayyar Afrika, ta yi kira ga Majilasar Ɗinkin Dunia, da ta ɗauki matakan ladabtar da duk mutanen da a ka samu, da hannu a cikin warware tumƙar da ake , domin kawo ƙarseh rikicin ƙasar Cote D `Ivoire.

AU, ta yi wannan kira jiya, bayan ta gano cewar, a na fuskantar tafiyar haiwainiya, a shirye shiryen zaɓukan da a ka ambata gudanarwa kamin ƙarshen 31 ga watan oktober na wannan shekara.

Jikadan Nigeria, a komiti tsaro da kwantar da tarzoma na Au, Olusegun Akinsaya, ya bayanawa manema labarai cewar, a yayin da ya rage watani 5 rak, a shirya a zaɓen har yanzu, babu alamomi a zahiri masu nuna yiwuwar wannan zaɓe.

Ambasada Akinsanya, yi gayyaci ɓangarori daban daban masu adawa da juna, a Ivory Coast, da su yi iya ƙoƙarin su domin tabatar da yarjejeniyoyin da su ka cimma daidaito kan su, wanda kuma su ka samu amincewa, daga Au da Majalisar Ɗinkin Dunia.