1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan Afirka zai jagorancin WHO

Mohammad Nasiru Awal
May 26, 2017

Bunkasar tattalin arzikin Afirka da nada dan Afirka a matsayin shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO sun dau hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2dcBo
Tedros Adhanom Ghebreyesus
Sabon shugaban hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom GhebreyesusHoto: Picture alliance/dpa/M. Kappeler

A karon farko dan Afirka zai jagorancin hukumar lafiya ta duniya WHO inji jaridar Süddeutsche Zeitung. Ta ce dan kasar Habasha ko Ethiopia Tedros Adhanom Ghebreyesus da ya kasance abin koyi ga 'yan siyasa amma kuma da yawa ke wa kallon karen farautar gwamnatin kama karya ya zama sabon shugaban hukumar lafiya WHO. Shi dai Tedros Ghebreyesus dan shekaru 52 ya taba rike mukamin ministan kiwon lafiya a kasar Habasha inda a lokaci aka zarge shi da boye gaskiyar barkewar cutar kwalera. Ya samu goyon bayan tsohon daraktan hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta Amirka a zaben neman shugaban WHO. Yana da digirin-digirgir a fannin kiwon lafiya al'ummomin yankuna karkara. 

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta buga labarin game da bunkasar tattalin arzikin nahiyar Afirka ta na mai cewa yawan zuba jari kai tsaye da karin bukatun kayayyaki a cikin gida sun taimaka wajen samun wannan cigaba. Ta ce tattalin arzikin nahiyar Afirka zai sake bunkasa daga kashi 2.2 cikin 100 da aka samu a shekarar 2016, a bana bunkasar za ta kai kashi 3.4 cikin 100, bisa alkalumman da bankin raya kasashen Afirka da kungiyar OECD da kuma shirin raya kasashen Afirka na Majalisar dinkin Duniya suka bayar. A badi wato 2018, hukumomin na kasa da kasa sun yi hasashen cewa Afirka za ta samun bunkasar tattalin arziki da za ta kai kashi 4.3 cikin 100. 

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta leka kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ta na mai cewa kasar ita ce kan gaba a duniya wajen yawan mutanen da ake kora daga yankunansu na asali a shekarar da ta gabata. Jaridar ta ce a shekarar 2016 babu wata kasa a duniya da aka kori mutane daga yankunansu na asali da ta kai Jamhuriyar demokradiyyar Kwango, inda a bara aka yi rajistar mutane dubu 922 da aka tilasta musu tashi daga yankunansu. Sannan a watannin farko na wannan shekarar an kori kimanin dubu 800.