1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan bindiga ya bude wuta a Turkiyya

January 1, 2017

A Turkiyya an shiga cikin sabuwar shekara da bacin rai bayan da wani dan bindiga ya kai hari a wani gidan rawa da ke a birin Istanbul wanda a cikin mutane 39 suka mutu kana wasu 69 suka jikkata.

https://p.dw.com/p/2V6Zy
Türkei Istanbul - Sanitäter transportieren verletzte nach Angriff auf Nachtclub
Hoto: Reuters/Stringer

Ministan cikin gida na Turkiyya ya ce daga cikin wadanda suka mutu har da 'yan kasashen waje guda 19. Wanda ya kai harin  ya yi shigar burtu a gidan rawar sannan ya  bude wuta a kan jama'ar daf da lokacin ake yin bukukuwan shiga sabuwar shekara ta 2017. Hukumomi a kasar dai sun ce suna ta kokari wajen damke wadanda ke da hannu wajen shirya wannan hari yayin da a share guda kasashen duniya ke cigaba da aikewa da sakonninsu na jaje ga mahukuntan Turkiyya din.