1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan Kasa ?

YAHAYA AHMEDNovember 23, 2005

Wani haifaffen kasar Najeriya na gwagwarmayar kare matsayinsa na kasancewa dan kasar Jamus, gaban kotun kundin tsarin mulkn kasa da ke birnin Karlsruhe.

https://p.dw.com/p/BvUJ
Kotu
KotuHoto: dpa

A karamar hukumar Pforzheim da ke jihar Baden Würtemberg ne haifaffen kasar Najeriyan yake da zama. Zargin da jami’an karamar hukumar ke yi masa, shi ne ya shara musu karya wajen neman zamowa dan kasar Jamus da ya yi. Amma a lokacin, ba a gano karyar tasa ba, sai bayan da ya sami duk cikakkun takardunsa na dan kasa. A ganin karamar hukumar dai, haifaffen Najeriyan, ya yaudari jami’anta ne yayin da ya bayyana musu cewa, yana aiki kuma zai iya ciyad da iyalinsa. Game da hakan ne kuwa, aka amince da ba shi fasfot da takardar shaidar dan kasar Jamus.

Sai can daga baya ne aka gano cewa, ashe ba shi yake aikin ba. Wani ne ya bai wa takardunsa yake aiki da sunansa, a ma’aiakatar da ya sanar da hukuma cewa nan yake aiki. To game da hakan ne dai, hukumar ta yanke shawarar janye takardun zamowa dan kasar Jamus da aka ba shi.

Shi ko gogan, bai yi wata wata ba, sai daukaka kara gaban kotun kundin tsarin mulkin kasa, don nuna adawarsa ga matakin da karamar hukumar ta dauka. Ita karamar hukumar dai ta dage kan cewar, tun da yaudara ya yi ya sami takardun, to yanzu da aka gano magudin da ya yi, dole ne a janye su, a a soke matsayinsa na kasancewa dan kasar Jamus.

Sai dai alkalan kotun, ba za su iya yanke hukunci kai tsaye kamar yadda karamar hukumar ke bukata ba, inji Wilefried Hassemer, shugaban reshen da ke kula da wannan batun. Wajibi ne su yi nazari mai zurfi a kansa, su kuma tabbatar ko wane hukunci suka yanke, ya dace da ka’idojin kundin tsarin mulkin kasa.

Kuduri mai lamba 16 na kundin tsarin mulkin kasar dai, ya hana janye wa duk wani bajamushe hakkinsa na zamowa dan kasa. A kan wannan kudurin ne kuma, lauyoyin haifaffen kasar Najeriyan suka dogara, wajen neman kotun ta soke hukuncin da karamar hukumar ta yanke. Sun kara nanata cewa, babu wani shafi na kundin da ke ba da izinin janye wa duk wani bajamushe `yancinsa na kasancewa dan kasa ko da ma, yaudara ya yi wajen samun takardun zamowa dan kasar. To ko da ma, alkalan sun bai wa karamar hukumar Pforzheim din gaskiya, suka kuma ci gaba da aiwatad da shirinsu, yaya makomar iyalin shi mutumin zata kasance ? Tun da su ma, wato matansa da yaransa, sun zamo Jamusawa saboda takardar da uban ya fara samu. Babu dai wata doka da z ata sa su am a janye musu takardunsu. Lauyoyin sun kara bayyana cewa, idan aka janye masa takardunsa na kasancewa dan kasar Jamus, ba shi da inda zai nufa kuma. Saboda, kafin ma a ba shi takardun kasar Jamus din, sai da ya mika duk tsoffin takardun shaidar dan kasa ta Najeriya da yake da su ga hukumomin kasarsa ta haihuwa.

A nasu bangaren, lauyoyin gwamnatin tarayya da na jihar Baden-Württemberg sun yi watsi da wannan ra’ayin. Sun ce, hanyoyin da ya bi wajen samun takardun sun saba wa dokar Jamus. Sabili da haka ne suke ganin, ba shi ma da izinin yin matashiya da ka’idojin kundin tsarin mulkin kasa.

A lokacin da aka tsara kundin tsarin mulkin kasar Jamus a shekarar 1949 dai, an zartad da kuduri mai lamba 16 ne, saboda hana wata hukuma yin kwaikwayo da salon `yan mulkin Nazi, inda suke soke wa jama’a da dama `yancinsu na zama `yan kasar Jamus, kawai saboda wariya da kabilanci.

Ana dai kyautata zaton cewa, sai cikin watan Maris ko Ifirilu na shekarar badi ne kotun zai yanke hukunci a kan wannan batun.