1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Amurka da kasar Libya

May 16, 2006
https://p.dw.com/p/BuyE

Amurka zata maida huldar jakadanci da kasar Libya tare kuma da tsame ta daga jerin kasashen da ta yiwa lakabi masu daurewa ayyukan taádanci gindi. Amurkan dai na saka wa shugaban kasar Libyan Moammar Ghaddafi ne wanda ta ce ya kawar muggan makaman sa na kare dangi sannan kuma yana bada cikakken hadin kai wajen farautar yan tarzoma. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice tace wannan kwakwaran sakamako ne mai alfanu wanda ya biyo bayan shawarar da gwamnatin Libya ta yanke na yin watsi da akidar tarzoma da kuma lalata makaman ta masu hadari. A yayin da Amurkan ke sakanyawa kasar Libya a waje guda kuma ta haramta sayarwa kasar Venezuela makamai saboda abin da ta baiyana da cewa rashin bada hadin kai daga shugaban kasar Hugo Chavez na yaki da ayyukan tarzoma. Wadannan matakai sun zo ne a daidai lokacin da kasashen yammacin turai ke shawarta bani gishiri in baka manda domin sulhunta rikicin iran na yaduwar makaman nukiliya. Amurka na bukatar kasashen Iran da koriya ta arewa su yi koyi da kasar Libya ta kawo karshen shirin su na mallakar makaman nukiliya.