1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Biranen Duniya

September 28, 2004

Ana samun ci gaba wajen raya makomar zamantakewar jama'a a manyan garuruwa da biranen kasashe masu tasowa fiye da yadda lamarin yake dangane da kasashe masu ci gaban masana'antu

https://p.dw.com/p/Bvg8

A hakika wajibi ne kasashe masu ci gaban masana’antu su dawo daga rakiyar akidarsu ta mai-bayarwa-da-mai-karba a dangantakarsu da kasashe masu tasowa. Iya yi na kasashe masu ci gaban masana’antu, shi ne ya sanya har yau kwalliya ta kasa mayar da kudin sabulu dangane da matakai iri dabam-dabam da ake dauka domin raya kasashe masu tasowa. An ji wannan bayanin ne daga Ulrich Nitschke, wakilin wata hukumar ba da shawara akan manufofin raya kasa dake nan Jamus a lokacin taron biranen duniya a Barcelona ta kasar Spain. Ya ce a yayinda mutane, a kasashe masu ci gaban masana’antu, ke dada kosawa da al’amuran siyasa, suna masu rowar kuri’unsu a lokacin zabe, a kasashe da dama dake tasowa da wadanda ke da matsakaicin ci gaban masana’antu mutane kan yi cincirindo domin amfani da damar da mulkin demokradiyya ya tanadar musu na jefa kuri’a da bayyana matsayinsu na siyasa, kazalika ba sa sako-sako wajen shiga a rika damawa da su a matakai na raya makomar birane ko garuruwarsu. Babban misali a nan shi ne birnin Porto Alegre na kasar Brazil, wanda tun a shekarar 1996 ake yaba masa da zama babbar alkaryar demokradiya ta duniya, ganin yadda mazauna birnin ke ba da cikakkiyar gudummawa a matakan da suka shafi raya makomar zamantakewar jama’a a cikinsa. Wadannan mutane sun farga da muhimmancin dake akwai wajen kawar da najasa da tsaftace kewayen muhallin zamansu. A Porto Alegre jama’a ne ke tsayar da shawara akan abubuwan da ya kamata a kashe kudi kansu saboda ikon da suke da shi na tofa albarkacin bakinsu akan kasafin kudin karamar hukumar yankin. Wannan rawa da al’umar Porto Alegre ke takawa ta taimaka wajen kayyade miyagun laifuka a birnin da kuma fayyacewa a fili wuraren da kudaden karamar hukumar ke kwarara. Kimanin kashi 98% na mazauna birnin suka iya rubutu da karatu kuma ayyukan kiwon lafiya na tafiya salin alin ba tare da wata tangarda ba. Wannan ci gaba da birnin na Porto Alegre da sauran birane ke samu a kasashe masu tasowa ya ba wa wasu birane da kananan hukumomi na Jamus kwarin guiwar yin ko yi da su. Ma’aikatar cikin gida ta jihar Northrhine-Westfaliya na hadin guiwa da asusun Bertelsmann domin rufa wa garuruwan Hamm da Hilden da Castrop-Rauxel wajen kyautata makomar zamantakewar jama’a a cikinsu. Koyan darasi daga juna shi ne ainifin abin da hukumar ba da shawara akan manufofin raya kasa ta saka a gaba a cewar darektanta Ulrich Nitschke. A shekara ta 2006 ne za a gudanar da taron birane na duniya a Vancouver ta kasar Kanada, mai yiwuwa kafin sannan al’amura sun kara kyautatuwa a dangantakar birane da kuma koyan darasi daga kasashe masu tasowa.