1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Faransa da Kasashen Afurka

November 15, 2004

Rikicin kasar Cote d'Ivoire sai dada tsamari yake yi, a yayinda a daya bangaren kuma ake kara shiga mawuyacin hali a dangantakar Faransa da kasashen da ta rena a nahiyar Afurka

https://p.dw.com/p/Bved

Shi dai shugaba Laurent Gbagbo, wanda a zamanin baya ake yaba masa da sukan lamirin manufofin gwamnati, a yanzun ya wayi gari a matsayin dan kama-karya, wanda ya dogara kacokam akan matasa ‚yan ta-kife domin tabbatar da angizon mulkinsa. A yayinda a sauran sassa na Afurka aka saba magudi a zabe, a can Cote d’Ivoire wani sabon salo na kabilanci ne aka fake da shi domin hana masu kalubalantar Laurent Gbagbo shiga zabe da kuma tauye hakkin magoya bayansu a manufofi na cikin gida. Daya matsalar kuma ita ce kasancewar a kasar ta Cote d’Ivoire, daidai da sauran kasashen Afurka, tattalin arzikinta ya dogara ne kacokam akan kasashen ketare ta yadda wasu ‚yan tsiraru ne kadai ke cin gajiyarsa, lamarin da ba shakka yake barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’ar kasa. Cibiyoyin kudi, irinsu bankin duniya da asusun bayar da lamuni na IMF da kasar faransa da kuma gaggan kamfanoni na kasa da kasa sune ke jan akalar tattalin arzikin Cote d’Ivoire, kuma kananan manoma sune suka fi fama da radadin tsauraran sharuddan da asusun IMF ya shimfida dangane da sabbin manufofin cinikin koko da gahawa da auduga da roba da kasar ke fitarwa zuwa ketare. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar masu boren dake ta da kayar baya yanzu haka a kasar ta yammacin Afurka, a baya ga manufofin na siyasa suka dage akan ganin lalle sai an yi raba daidan arziki da kuma mukamai a kasar. Ita dai Cote d’Ivoire ta zama kyakkyawan misali a game da al’amuran kan tabarbare a shiga fama da neman bakin zaren warwaresu idan har an sa kafa an yi fatali da kamanta adalci a zamantakewar jama’a da huldodin rayuwa ta yau da kullum. A yanzu haka kasar, wacce a zamanin baya ta zama tamkar abin koyi ga sauran makobtanta, tana fama da yamutsi, wanda tasirinsa ka iya yaduwa ya hada da makobtan nata. Rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a Cote d’Ivoire ya zame wa kasar Faransa kayar kifi a wuya. Domin kuwa babu wanda ya san tahakikanin alkiblar da kasar ta Faransa ta fuskanta dangane da gwamnatin Gbagbo saboda magana da take yi da baki biyu-biyu. Daya daga cikin dalilan haka kuwa shi ne kudurin da kasar ta yanke na kin katsalandan kai tsaye a al’amuran cikin gida na kasashen Afurka da ta rena, a karkashin tsofon shugaba Francois Mitterrand, a yayinda shi kuma shugaba Chirac ke Allah Waddai da duk wani mataki na kwatar mulki da karfin bindiga, lamarin da neman tabarbara ma’amallar Faransar da kasashen da suka taba wanzuwa karkashin mulkin mallakarta a Afurka.