1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Iran da Turai da Amurika

Sadissou YahouzaAugust 5, 2009

Bayan rantsar da shugaba Mahmud Ahmadinijad minene makomar dangantaka tsakanin Iran da ƙasashen yammacin duniya ?

https://p.dw.com/p/J4Bv
An rantsar da Mahmud Ahmadinedjad a matsayin shugaban ƙasar IranHoto: AP

Tun shekaru da dama, ƙasashen duniya suka ɗorawa Iran ƙafan zuƙa, a dalili da shirinta na mallakar makamaan nukiliya.

Hulɗoɗin sun Ƙara gurɓacewa tsakanin ɓangarorin biyu, bayan zaɓen shugaban ƙasa, na ranar 12 ga watan Juni, wanda ya ba shugaban Mahamud Ahmadinedjad damar yin tazarce.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na daga sahun shugabanin da suka yi Allah wadai ga sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Iran a watan juni na wannan shekara, sannan ta bayyana takaici agame da abinda ta kira take haƙƙoƙin bani adama da hukumomin Iran ke yi mussamman ga masu zanga zangar nuna adawa ga zaɓen.Merkel ta cigaba da cewa:

Na san mahimmancin ´yancin ɗan adam,ni ganau ce ba jiyau ba, tun lokacin da Jamus ta rabu gida biyu. Na san mahimmancin baiwa ɗan adam ´yanci da kuma kula da bukatocinsa,a duk inda yake rayuwa.

Itama ƙasar Amurika ta daɗe da shiga ƙafar wando guda da Iran to amma.saidai bayan zaɓen shugaban ƙasa Barack Obama ya miƙa goran sulhu ga hukumomin Teheran.

Shima Obama ya bayyana damuwa agame da yadda Iran ta ɗauki matakan murƙushe ´yan adawa.

A wani taro da suka kira watan Juli da ya gabata,a ƙasar Italiya,shugabanin ƙasashen mafi ƙarfin tattalin arzki a duniya sun jaddada tofin Allah tsine ga kalamomin da shugaba Mahmud Ahmadinejad kewa ƙasar Isra´ila.

Shugaba Barack Obama na Am urika ya bayyana gamsuwa a game da matakin na bai daya da suka cimma:

Abunda muke buƙata shine muka samu, wato cimma matakin haɗin gwiwa ta fannin yin Allah wadai ga ƙuntatawar da Iran kewa ´yan adawa da jami´an diplomasiya da kuma tauye yancin ´yan jarida.Saidai ina fata mu samu haɗin kai da ƙasar Rasha a wannan mataki da muka ɗauka.

ƙasahen G8 sun jaddada matsayinsu na yin Allah wadai ga shirin Iran na mallakar makaman nukiliya.Sun ba ƙasar wa´adin ƙarshe, har zuwa wata mai kamawa na satumba domin tayi watsi da wannan shiri.

Idan kuma hukumomin Teheran sukayi kunen ƙashi G8 ta yi barazanar tsuke takunkumin da ta sakawa Iran.

Saidai a wani mataki mai kama da saidai a kashe tsohuwa kan daddawarta, shugaba ƙasar Iran a jawabin da ya gabatar yau, a Majalisar dokoki albarkacin rantsar da shi a matsayin zaɓɓaɓen shugaban ƙasa ya ce shirinsa na nukiliya babu gudu babu ja da baya.

saidai bayan matsayin lamba daga waje shugaban na shan ƙaimi har daga cikin gida.

A wata ziyara da ta kawo nan gidan redio DW, Sherin Ebadi mace mai kamar maza, ´yar ƙasar Iran, wada ta taɓa samun tukwicin Nobel Price, ta yi kira ga ƙasashe duniya cewa ,idan zasu sakawa Iran takunimuin ta kamata ya kasance ta fannin siyasa amma kar ya shafi rayuwar jama´ar ƙasar:Takunkumi ta fannin siyasa a gani na ya fi tasiri, misali ƙasashen turai su janye opisoshin jikadancinsu, su maye gurbinsu da ƙananan opisoshin jikadanci.Wannan mataki ba zai shafi tallaka ba, amma su magabatan, zasu ji a jika.

Takunkumi ta fannin siyasa ko ta fanin tatalinarzii ne dai a yau ne aka rantsar da Ahmadinejad Nijad a matsayin zaɓɓaɓen shugaban ƙasar Iran , shin ƙaƙa ma´maila zata kasance tsakaninsa da ƙasashen Turai da Amurika ?

Mawwalafi: Matthias/ Yahouza

Edita: Aliyu