1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

031010 D Russland Beziehungen

September 30, 2010

Ana ci gaba da samun ingancin dangantakar Rasha da Jamus bayan haɗewar Jamus a 1990.

https://p.dw.com/p/PREY
Tutocin Jamus da Rasha.Hoto: DW

Tun bayan sake haɗewar gabashi da yammacin Jamus shekaru 20 da suka gabata ne dai ake ci gaba da samun ƙarfafuwar dangantaka musamman a fannin tattalin arziƙi tsakanin Haɗaɗɗiyar ƙasar Jamus da Rasha, wadda ta taka rawar gani wajen haɗe ɓangarorin biyu.


Shugaba Mikhail Gorbachev na Tarayyar Soviet ya kawo ziyararsa ta farko a birnin Bonn a ranar 9 ga watan Nuwamban shekarar 1990, wasu 'yan makonni bayan sake haɗewar gabashi da yammacin Jamus . A yayin wannan ziyara Shugaban gwamnatin Jamus na wancan, lokaci Helmut Kohl da shugaban na Rasha sun rattaba hanu kan yarjejeniyar maƙwabtaka da yin aikin haɗin-gwiwa tsakanin ƙasashen biyu. Kohl ya ce wannan na zaman wani sabon babi. Ya ƙara da cewa: "Za mu yi aiki da wannan yarjejeniya ba tare da barinta a rubuce ba. Mu a matsayinmu na Tarayya da kuma gwamnatin Jamus muna buƙatar ƙarfafa dangantaka a dukan fannoni, kama daga tattalin arziƙi, da siyasa da musayar al'adu da bincike da fasaha zuwa musayar ilimi tsakanin matasa daidai da wannan yarjejeniya.

Tun daga shekarar 1990 ne kuma Jamus da Tarayyar Soviet suka kama hanyar ƙarfafa dangantakarsu babu ƙaƙƙautawa. Tun daga lokacin yaƙin cacar baki a shekarun 1960 ne dai, Jamus ta ƙirƙirar da dangantakar tattalin arziƙi tsakaninta da Tarayyar Soviet. Ko shakka babu dangantakar Shugaba Gorbachev da Kohl ta taka rawar gani wajen ƙarfafa danƙon zumuncin tsakanin ƙasashen biyu. Dangantakar ta ma ƙara danko ne a lokacin da tsohon shugaba Vladimir Putin, magajin Boris Yelsin yayi aiki a matsayin jami'in ma'aikatar leƙen asirin Rasha KGB a nan Jamus inda ya samu ƙwarewa a harshen Jamusanci. Ya ce: "Yanzu Jamus ta zama muhimmiyar abokiyar aikin Rasha a fannin tattalin arziƙi, kuma muhimmiyar aminiyarmu, abokiyar shawara a fannin siyasa."

Russland Deutschland Wissenschaft Putin besucht Expedition Lena 2010 auf Insel Samoilowski
Vladimir Putin, na biyu daga hagu yayin wata ziyara a Jamus.Hoto: AP

An dai samu kyakyawan dangataka tsakanin Putin da Schroeder wanda za a iya cewa shi ne shugaban gwamnatin Jamus mafi kusanta da Rasha. To amma ba dukannin ƙasashen Turai ne ke nuna jin daɗinsu game da dangantakar da ke tsakanin Jamus da Rasha ba. Akwai masu sukan gwamnatin Jamus bisa abin da suka kira take-takenta na yin wasti da buƙatun ƙananan ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai domin samun biyan buƙatar kasuwanci da kuma iskar gas daga Rasha. A baya ga haka babu wani tsoƙaci da Jamus ke yi game da rashin bin tsarin dimukuraɗiya a Rasha.

Tun bayan da ta kama ragamar shugabancin Jamus ne dai, Shugabar gwamnati, Angela Merkel ke ƙoƙarin nesanta kanta da Rasha. Sai dai ma ta fito ƙarara ta yi suka ga ƙasar Rasha game da rashin bin tsarin dimukuraɗiya-abin da ya harzuƙa Shugaba Vladimir Putin. To sai dai a yayin wata ganawa da ta yi da Shugaba Dmitry Medvedev a watan Yulin wannan shekara, Merkel ta bayyana irin kyakyawar dangantakar da ke akwai tsakanin Rasha da Jamus, a dangane da matsalar tattalin arziƙi da ta addabi duniya. Ta ce: "A haƙiƙa haɗin-kan da Jamus ta samu shekaru 20 da suka gabata ba ma a Jamus da Ƙungiyar Tarayyar Turai ne kaɗai ya kyautata rayuwa ba. Ya kuma kyautata dangantakar Jamus da sauran ƙasashe masu faɗa a ji a duniya, waɗanda Rasha ke ɗaya daga cikinsu. Yanzu muna da dangantakar kut da kut da Rasha a baya ga haɗin-giwar siyasa da kuma yin aiki tare tsakanin ƙungiyar ƙasashe masu arziƙin masana'antu, wato G8 da kuma ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi a duniya, wato G20.

Bildgalerie Jahresrückblick 2008 Juni Deutschland Russland
Angela Merkel da Dmitry Medvedev.Hoto: AP

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal