1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DANGANTAKAR KASASHEN JAMUS DA FANRA DA AMURKA BAYAN YAKIN IRAQI.

Ibrahim saniJanuary 15, 2004
https://p.dw.com/p/BvmZ
Bayan rashin jituwa da rashin fuskantar juna da aka samu a tsakanin kasar Amurka da Jamus a daya hannun kuma da Faransa kann hawa kujerar nakin da sukayi wajen marawa kasar ta Amurka baya kann yakin kasar Iraqi,a yau alhamis rahotanni sun nunar da cewa dangantaka a tsakanin kasashen ta fara hawan turbar kyautatuwa na kara kulla zumunci.
Kafafen yada labaru na Faransa sun rawaito ministan harkokin wajen kasar Dominique de Villepin na fadin cewa abubuwan da suka faru a baya a tsakanin kasashen dangane da yakin kasar ta iraqi ya wuce sai dai kuma a kori gaba.
Bisa kuwa kyautata dangantaka a tsakanin kasar sa da kasar ta Amurka ministan cewa yayi yanzu ma aka fara,musanmamma ta fannin yaki da tsageru masu tsattsauran raayi.
Mr Dominique yaci gaba da cewa,to amma duk da kyautata dangantaka da kasashen biyu suka dukufa da yi,dole ne a samu rashin jituwa ta wasu fannnoni na rayuwa da suka hada da bin ka,ida kamar yadda doka ta tanadar da nuna adalci da kuma warware abubuwa da suka sarke ta hanyar neman shawarwari.
Bisa kuwa kyautata dangantaka a tsakanin juna a yau ministan tsaro na Faransa Michele Alliot Marie zai kai ziyarar aiki izuwa kasar Amurka,wanda itace ta farko a tun bayan da kasar ta Amurka ta afkawa kasar iraqi da yaki a watan maris na shekarar data gabata. A lokacin ziyarar ana sa ran ministan zai gana da takwaransa na Amurka Donald Rumsfeld da kuma Condoleeza Rice mai bawa shugaba Bush shawara ta fannin tsaro,kann kyautata dangantakar harkokin tsaro a tsakanin kasashen biyu.
A hannu daya kuma a can birnin Berlin na tarayyar Jamus,rahotanni sun shaidar akwai alamun mahukuntan kasar ka iya canja matakin da suka dauka da farko na kin tura sojin su izuwa iraqi bayan yaki,ba don komai ba kuwa sai don kara gyara dangantaka a tsakanin kasashen biyu wacce tayi tsami sakamakon yakin kasar ta iraqi.
Wata jaridar kasar mai suna Die Welt ta rawaito cewa sakamakon wani taro da shugaban gwamnati Gerhard schroder ya gudanar da wasu mambobin kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin kasar,a yanzu haka kasar na tunanin tura wasu jiragen kasar izuwa kasar ta iraqi don gudanar da aiyuka,amma kuma a karkashin lemar mdd.
Schroder yaci gaba da cewa,Jamus za kuma taci gaba da taimakawa kungiyyar tsaro ta Nato da yanzu haka ruwa tsundun wajen gudanar da aikin tsaro a kasar ta iraqi bayan yakin.
A wata sabuwa kuma wani kamfanin ciniki da masana,antu na Jamus yayi marabi da matakin da Amurka ta dauka na kyale wasu kamfaninnika daga kasashen da suka hau kujerar nakin yakin kasar ta iraqi neman kwangilar sake gina kasar,da cewa wannan mataki ne mai kyau daya dace. A daya bangaren kuma wata cibiyar yan jaridu mai zaman kanta ta soki lamirin sojojin kasar ta Amurka da yin shakulatin bangaro na kashe wasu yan jaridu biyu da wasu sojin kasar sukayi ta hanyar saka bom a otal din Palestine dake birnin Bagadaza.
Cibiyar yan jaridun ta kuma kara da cewa bayan rasa rayuka da akayi wasu kuma sun jikkata,amma kuma har yanzu mahukuntan kasar ta Amurka sunki suyi wani abin azo a gani dangane da hakan.