1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Kasashen Kungiyar Tarayyar Turai Da Kasashe Masu Tasowa

May 28, 2004

Bisa ga dukkan alamu a yanzun za a shiga wani sabon yanayi a game da dangantakar kasashen Turai da kasashe masu tasowa sakamakon karbar sabbin kasashen da aka yi a KTT

https://p.dw.com/p/BvjF
Tutar Kungiyar Tarayyar Turai
Tutar Kungiyar Tarayyar Turai

Dukkan kwararrun masana da ‚yan siyasa da wakilan kungiyoyin taimako masu zaman kansu sun hakikance cewar za a samu canji a dangantakar kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da kasashe masu tasowa sakamakon sabbin kasashe goma na gabacin Turai da suka shigo tutar kungiyar. A lokacin da take bayani a game da makomar dangantakar sassan biyu Heike Pörksen daga ma’aikatar taimakon raya kasashe masu tasowa nuni tayi da cewar mai yiwuwa a samu canji dangane da kasashen da aka saba ba su fifiko wajen gabatar da taimakon raya kasa. A halin yanzu haka dai ana tattaunawa a game da sabbin manufofin makobtaka da juna, wanda lamari ne da ya shafi sabbin makobtan kasashe dake da iyaka kai tsaye da kasashen KTT sakamakon bunkasarta zuwa kasashe 25. Su dai sabbin kasashen kungiyar, ta la’akari da tarihinsu na wanzuwa, sun fi kaunar ganin an ba da fifiko ga manufofin tsaro da na tattalin arziki da kuma kyautata tsarin demokradiyya a kasashe masu tasowa. An saurara daga bakin Marian Caucik, shugaban gamayyar kungiyoyin taimako masu zaman kansu a kasar Slovakiya yana mai bayanin cewar, sabbin wakilan kungiyar ta tarayyar Turai suna sha’awar kara karfafa hadin kansu da kasashen da suka saba ma’amalla da su tun a zamanin baya. Za a kuma ba da la’akari sosai da kasashen da suka biyo-bayan rusasshiyar Tarayyar Soviet. Kazalika da kasashen Afurka da na Asiya. Caucik ya kara da cewar zai zama babban kuskure idan aka yi sako-sako da al’amuran kasashen Afurka ko na Asiya sakamakon bunkasar yawan kasashen KTT. Sabbin kasashen kungiyar na da nauyi daidai da tsaffin kasashenta a game shirinta na taimakon raya kasashe masu tasowa ko da yake a halin da ake ciki yanzu gudummawar da zasu iya bayarwa ba ta taka kara ta karya ba. Nan gaba za a kara yawan kudaden gudummawar, duk da cewar ba abu ne da zai dadada wa al’ummominsu ba, ta la’akari da matsalolinsu na cikin gida. Amma duk da haka kasashen na iya ba da gudummawa ta fasaha, ba lalle sai taimakon kudi ba. Wadannan kasashe suna da cikakkiyar masaniya a game da matsalolin kasashe masu tasowa dangane da hali na koma baya da su kansu suka taba kasancewa a ciki. Gaba daya dai ba wanda ya san yadda makomar dangantakar zata kasance tsakanin kasashen na KTT da kasashe masu tasowa. Ita dai kungiyar tun da dadewa take ba da la’akari da bukatunta ta fuskar tsaro da manufofin ketare kuma ba za a samu sauyi game da hakan nan ba da dadewa ba.