1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Kungiyar Tarayyar Turai da Kasar Bailorushiya

June 1, 2004

Shugaba Lukashenko na Bailorushiya ya ce kasarsa ba kungiya ce ta taimakon jinkai ba kuma a saboda haka wajibi ne ta samu hadin kan kudi daga kasashen Turai domin yaki da bakin haure

https://p.dw.com/p/BvjE
Shugaba Alexander Lukashenko na Bailorushiya
Shugaba Alexander Lukashenko na BailorushiyaHoto: AP

Ita ma dai Kungiyar Tarayyar Turai, daidai da kasar Bailurushiya, ba kungiya ba ce ta taimakon jinkai kuma ba zata yarda ta rufa wa ‚yan mulkin kama karya irin shigensu shugaba Alexander Lukashenko baya ba. Ka da a manta Lushenko, har yau yana kan bakansa na aiwatar da danyyen mulki da fatattakar abokan hamayya domin tsaresu a gidajen kurkuku ko kisan su gaba daya. Ba ya kaunar ‚yan jarida dake kalubalantarsa da laifuka na cin hanci da rashin sanin makama wajen tafiyar da al’amuran tattalin arzikin kasa. Ta la’akari da haka ana iya cewar shugaban na kasar Bailorushiya ko kadan bai cancanci samun wani taimako ko da na sinsin kwabo ne daga kasashen yammaci ba.

Hakkun ne cewar akwai ‚yan gudun hijira masu tarin yawa musamman daga kasashen Asiya dake amfani da kasashen Rasha da Bailorushiya domin shigowa yammacin Turai kuma a halin yanzu haka ita Bailorushiya tana da iyaka kai tsaye da KTT a yammacinta tun bayan karbar karbar karin kasashe na gabacin Turai da aka yi a kungiyar. Amma hakan bai isa ya zama dalilin da zai sanya danka masa miliyoyin dala, kamar yadda yake bukata, domin mara wa haramtacciyar gwamnatinsa ba. A hakika ma dai babu wani abin dake shaidar cewar dan kama karyar zai yi amfani da wadannan kudade ne domin hana tuttudowar bakin haure zuwa kasashen yammacin Turai. Duk wani sassaucin da za a nuna masa zai zama tamkar wata nasara ce ga Lushenko domin ci gaba da cin karensa babu babbaka. Shugaban, shi ne ainifin ummal’aba’isin tabarbarewar tattalin arzikin kasarsa. Hatta shugaba Putin na Rasha ya fara janye jikinsa daga Lukashenko, inda Rashan a yanzun take ci gaba da tsawwala farashin man da take sayarwa da kasar Bailorushiya duk da cewar farashin ya gaza na kasuwannin duniya. Karuwar farashin ce ta jefa shugaban cikin hali na kaka-nika-yi, kuma a sakamakon haka yake neman wata kyakkyawar madogara ta samun taimako daga kasashen yammaci yana mai billo da maganar yaki da bakin haure. Lukashenko ya sha bakin kokarinsa na kare makomar bangarori da dama na tsarin tattalin arzikin kwaminisanci daga rusasshiyar daular Tarayyar Soviet bisa manufar karfafa mulkinsa. Wannan mataki na sa shi ne ya kai ,kasar ya baro. A yayinda makobtan kasashe irinsu Rasha da na yankin Baltic ke samun bunkasar tattalin arziki, ita Bailorushiya sai dada fuskantar koma baya take yi.

A misalin shekara daya da rabi da suka wuce Lukashenko ya fito fili yana mai cewar nan ba da dadewa ba kasashen yammacin Turai zasu gurfana gaban Bailorushiya domin rokon hadin kai wajen yaki da safarar miyagun kwayoyi da bakin haure. Amma ga amamu murnarsa ta koma ciki, saboda kasashen na Turai ba su tinkareta da wannan batu ba, kuma ba zasu yi hakan nan gaba ba.