Dangantakar Masar da Hizbullah
April 28, 2010Wata kotu a ƙasar Masar ta ɗaure mutane 26 wadan da aka samu da laifin alaƙa da ƙungiyar Hizbullah, inda wasu kuwa aka ɗaure su da yunƙurin kai hari wa gwamnatin ƙasar ta Misira. Alƙalin ya yankewa 'yan wannan ƙungiyar waɗanda suka haɗa da yan ƙasar ta Masar da Sudan da Lebanon da Palsdinawa ɗauri na watanni shida izuwa ɗaurin rai da rai a gidan yari. Mutanen an kama su ne a tsakanin shekara ta 2008 da kuma 2009, inda ake zarginsu da laifin shirya kai hari a wuraren shaƙatawa na ƙasar da kuma yin liƙen asiri ma wata ƙasa ta ƙetare haɗe da samunsu da bama bamai. Shugaban ƙungiyar Hizbullah Hassan Nasarullah yace sam mutane basu da wani laifi, illa kawai ɗayan wanda aka tura domin ya taimakawa Palasɗinawa waɗawanda ke ƙarƙarme a yanken Gaza.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu