1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Paparoma da Afurka

April 4, 2005

Nahiyar Afurka ta fi kowace nahiya kewa da fama da radadin mutuwar Paparoma John Paul na biyu

https://p.dw.com/p/Bvcb
Marigayi Paparoma John Paul na biyu
Marigayi Paparoma John Paul na biyuHoto: dpa

Nahiyar Afurka ta fi kowace nahiya a duniyar nan tamu fama da radadin mutuwa, kuma mai yiwuwa a sakamakon haka ta fi kusanta da Allah. Domin kuwa akasarin yake-yaken da aka gudanar a cikin shekaru 50 da suka wuce sun wanzu ne a wannan nahiya. An sha fama da rahotannin kashe-kashen gilla da bala’in yunwa da yaduwar annoba ba kakkautawa. A halin yanzu haka cutar kanjamai ta zame wa nahiyar kayar kifi a wuya tare da halaka miliyoyin mutane, a baya ga zazzabin cizon sauro, wanda ya fi kanjamau illa, musamman ma ga yara kanana. A irin wadannan matsaloli zamu ga yawa-yawanci mujami’ar katolika ce ke kai doki ko dai ta gina tashoshin kiwon lafiya ko makarantu ko kuma akalla wata karamar tasha ta rediyo domin wayar da kan jama’a. Hakan ya taimaka a ko da yaushe zaka tarar da gidajen coci sun cika makil da mutane bisa sabanin yadda lamarin yake a sauran sassa na duniya. A sakamakon rawar da marigayi Paparoma John Paul na biyu ya taka a cikin shekaru sama da 25 da suka wuce aka samu ribanyar yawan mabiya darikar katolika zuwa kusan miliyan 100 a nahiyar Afurka. Kimanin kashi daya bisa goma na tafiye-tafiye 104 da Paparoma John Paul na biyu yayi zuwa kasashen ketare ya ya da zango ne a nahiyar Afurka, tare da bakin kokarinsa wajen ganin sakonsa ya yadu ya shiga kunnen kowa-da-kowa, ba mahalarta coci kadai ba. Kazalika ya kan tura manzanninsa domin sa baki a kokarin sasanta wasu daga cikin rikice-rikice masu tarin yawa da nahiyar Afurka ke fama da su. Paparoma John Paul na biyu, har ila yau, yayi bakin kokarinsa wajen ganin darikar katolika ba ta yi daura da bukatun kiristoci a nahiyar Afurka ba. An amince da wasu al’adun gargajiya, kamar kade-kade da raye-raye da wake-wake a zama na ibada a mujami’u da dama na katolika, kamar a kudancin Sudan. An samu matasa da dama da kan halarci kwasakwasai na addini a kokarin neman zama limaman coci, wanda ke taimaka musu wajen fita daga mawuyacin hali na rayuwa. Wasu bayanai sun ce bishop-bishop na Afurka suna daga cikin jami’an da suka fi yi wa Paparoma John Paul na biyu biyayya. Sun rungumi jawabansa a game da kayyade haifuwa da zub da ciki da hannu biyu-biyu. To sai dai kuma wani abin da wasu manazarta ke ganin zai iya zama alakakai ga mujami’ar katolika a nahiyar Afurka shi ne haramcin amfani da roba, wanda ke taimakawa wajen kara yaduwar cutar kanjamau. Akwai bukatar bitar wannan matsala, kamar yadda aka ji daga bakin wani matashi a Nairobin Kenya dake fama da radadin cutar yake kuma zargin cewar zai mutu a cikin kuruciyarsa.